Me ke haifar da yawaitar fyaɗe?

Assalam alaikum. Ina godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki.

Ina son mu fahimci daga inda ake fara fuskantar ƙalubalen fyaɗe da ake yi wa ƙananan yara mata da maza daga cikin gidajen mu da unguwannin mu. Matsalar da ta ke cigaba da zama gagarabadau a tsakanin al’umma da gwamnati, ba a Nijeriya kaɗai ba, har ma da sauran sassan duniya. Ko da yake ya danganta ga inda ta yi tasiri, da inda ta yi ƙaranci, saboda yadda tarbiyya da doka ke aiki.

Fyaɗe dai yana nufin saduwa da mace ko namiji ta hanyar jima’i ba da amincewar mutum ba, ko ta hanyar ƙarfi, tsoratarwa, ko ta bugarwa da sanya wani magani ko abin maye da zai gusar da hankalin mutum, ko ya sa barci da kasala mai nauyi, ko kuma ta hanyar yaudara. Masana da masu kare haƙƙoƙin ɗan Adam na ganin duk wata siga ta jima’i da za a yi da mace ko namiji, babba ko ƙaramar yarinya da ƙaramin yaro, ba da yardar su ko haɗin kansu ba, duk yana matsayin fyaɗe ne. Har ma da masu ganin ko da matar mutum ce, in ba da amincewar ta ba ne, shi ma fyaɗe ne.

Yara maza yawanci tun suna ƙanana a wasu wurare suna wasannin banza ko wasannin miji da mata, kuma ba a ganin hakan a matsayin wani abu, har ma a kai ga yaro namiji mai wayo ya riqa yi wa ƙananan yara mata wasa da al’aurar su, ba a ɗauki mataki ba. Har zuwa inda zai fara gwada amfani da ƙannensa yayin da shekarun sa suka fara haura bakwai zuwa goma, lokacin da wasu a cikin gidaje ke kallon abin da ƙuruciya, har suna cewa ai ya yi Washin Aska ne! Musamman bayan wani lokaci da warkewar kaciyarsa.

Ana samun irin wannan matsala ne, a inda iyaye masu ƙarancin tarbiyya ko waɗanda aka yi wa auren wuri, ba su samu kyakkyawar tarbiyyar da ta dace ba, har kuma suka fara samun yara, a cikin yanayin da tarbiyya ke ƙara taɓarɓarewar.

Cuɗanyar wasu yara maza da manyan yayu da suka balaga shi ma yana ƙara buɗe tunanin yaro ya taso da sha’awar yin abin da yake ji ana labari ko abin da yake gani na batsa a wayoyinsu. Haka ma a vangaren ‘ya’ya mata gwamutsa ƙananan yara mata da manya yana gurvatawa ƙananan tunanin su har ya fara kusantar da su wajen maza. Aiken yara ƙanana cikin maza a wuraren da ba na jama’a ba, shi ma yana sa su cikin tarkon wasu gurvatattun maza.

Yawaitar maza marasa aikin yi a cikin anguwa, yana sa ƙananan yara da ‘yan mata cikin haɗarin fuskantar fyaɗe, saboda balagaggun maza da ke zaune cikin anguwa babu damar yin aure ko samun mace a kusa da su, za su iya kai musu farmaki.

Tallace tallace da ake dorawa yara mata yana sa su shiga cikin manyan maza marasa tarbiyya da kamun kai, kuma su ma suna iya amfani da wannan damar su hurewa yaran kunne, har su aikata musu abin da ba su shirya saninsa ba.

Yawaitar magungunan ƙara sha’awa na maza da mata a tsakanin al’umma, babu sakayawa babu doka, shi ma yana jefa rayuwar yara cikin haɗarin fyaɗe. Domin duk namijin da ya sha magani bai samu yadda yake so ba to, idanunsa rufewa suke yi ya afkawa duk macen da ya samu kusa da shi. Don haka za ka yi ta jin ƙorafe-ƙorafen yi wa yara ƙanana fyaɗe a cikin kasuwanni, wuraren taruwar leburori, kangwayen gine-gine da sauransu.

Yawaitar shaye-shayen ƙwayoyi da sinadarai masu bugarwa na sa duk wanda ya ke cikin maye ba tare da sanin ina hankalinsa yake ba, ko kasa bambance daidai da ba daidai ba, shi ma yana iya sa shi ya afkawa duk macen da ya gani, komai kusancin sa da ita, ko da kuwa ‘yar cikinsa ce ko uwarsa mahaifiya.

Rashin amfani da tsauraran dokoki daga ɓangaren gwamnati ko hukumomin tsaro, ko kuma sasantawa a tsakanin iyaye, yana sa fyaɗe ya cigaba. Domin duk wanda ya saba, ba zai iya dainawa ba, sanin cewa, babu abin da zai same shi.

Wajibi ne kan iyaye su riƙa kula sosai da tarbiyyar yaransu, wanne irin kaya ko sutura suka sa? Wanne lokaci suka fi? Su waye ƙawayen ta? Wanne wuri ta ke zuwa talla? Akasari matsalolin da ake samu na fyaɗe yana da nasaba da sakaci da rashin samun cikakkiyar tarbiyya, ko tsawatarwar iyaye.

Wani lokaci kuma kamar yadda na ambata a baya, wasu yaran tun a gida ake samun yayunsu maza ko mata, ko kuma yaran makwafta suke fara koya musu lalata, ko yi musu fyaɗe. Hakan kuma na illa sosai ga tunanin yara da makomarsu. Ba na manta wa da labarin da wani abokina ya bani na yadda wata ƙanwar babansa da ke zawarci a gidan su, ta fara koya masa lalata, tun bai san mai ta ke yi ba. Wata kuma tun tana qaramar yarinya wani abokin yayanta da ke shiga gidansu yake yi mata wasannin da ba su kamata ba, har ma kuma ya fara yi mata fyaɗe, yana tsorata ta kada ta faɗa wa kowa.

Abubuwa da dama suna faruwa a tsakanin iyali da makwafta da ke haddasa jefa rayuwar yara cikin wani yanayi marar daɗi, da quruciyar su ko bayan sun girma, saboda rashin kula da rashin kula da sha’anin tarbiyyar yara. Irin haka ne yake sa yara su tashi da wasu irin halaye na jarabar sha’awa da bin maza ko halayyar neman mata, saboda abubuwan da suka riƙa faruwa da su tun suna yara ƙanana.

Allah Ya sa mu fi ƙarfin zuciyarmu, ya kuma tsare mu, ya tsare mana iyayenmu daga sharrin miyagun mutane.

Wasiƙa daga FATIMA MA’ASUMA, 09070905293 (Tes kawai).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *