Me ke sa fata baƙi a lokacin sanyi

Daga AISHA ASAS

Da yawa mutane kan yi tambayar me ya sa fata ke yin baƙi a lokacin sanyi, alhali babu rana da ke iya ƙona fatar. Sanannen abu ne, lokacin zafi fata kan shiga mawuyacin hali musamman ga ma’abuta yawo tsakiyar rana. Idan mai karatu zai iya tunawa, shafin kwalliya ya taɓa kawo darasi na musamman kan yadda rana ke taka rawa kan baƙin da fatarmu ke yi.

Sai dai a lokacin da wannan rana ta yi ƙaranta, akan samu wasu da ke yin duhu wani sa’ilin fiye ma da lokacin da ranar ta tsananta, wannan ke sa su tambayar me suke yi dake janyo hakan.

Uwargida akwai ababen da ba ki ɗauka komai ba waɗanda ki ke aikatawa da suke zama silar canzawar fatarki a yanayi na sanyi. Bari mu yi duba ga wasu daga ciki:

Man shafawa: Sanin kowa ne lokacin sanyi fata ta fi buƙatar ciyarwa ta ɓangaren mayukan shafawa, sanadiyar yawan saurin bushewa da ta ke yi wanda ke faruwa albarkacin yanayin na hunturu.

Da wannan ne mutane ke rufe ido wurin kallon illar mayuka, duk wani mai mautuƙar zai sanya fatar fita daga yanayin bushewa zuwa na matsƙi za su shafa don samun daidaito ga yanayin yadda suke jin jikinsu, ba tare da la’akari da zai iya cutar da fatar ko bata buƙatar irin sa, ko kuma zai iya vata launin fata. Da yawa fata kan yi baƙi a lokacin sanyi ta dalilin amfani da man da bai dace da fatarmu ba.

Wanka da ruwan zafi: Ruwan zafi na ɗaya daga cikin ababen da fata bata cika maraba da su ba, musamman idan suka kasance masu zafi sosai kamar yadda muke yi idan zafin ya tsananta. Wannan na iya zama sanadin duhun fata, musamman idan kina biye wa yanayin ƙaruwar sanyin wurin ƙara zafin ruwan.

Zai yi kyau idan ba za ki iya yi da masu sanyi ba, to a daure a yi amfani da masu ɗan ɗumi ba zafi sosai ba, matuƙar muna fatan kuɓutar da fatarmu ta wannan bangaren.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *