Ministan Harkokin Wajen Sin ya tattauna ta wayar tarho da Sakataren Harkokin Wajen Amurka game da hulɗar ƙasashen biyu da kuma batun Ukraine

Daga CRI HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar, Wang Yi, a ranar Asabar ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, game da hulɗar dake tsakanin Sin da Amurka da kuma batutuwan dake shafar Ukraine bisa gayyatar da Blinken ya yi masa.

Wang ya ce a halin yanzu, babban abinda hulɗar dake tsakanin Sin da Amurka za ta fi mayar da hankali shine, batun daga matsayi da kuma aiwatar da yarjejeniyoyin da shugabannin ƙasashen biyu suka cimma matsaya kansu a taron da suka gudanar ta kafar bidiyo, ya ƙara da cewa, ƙasar Sin ta bayyana matuƙar damuwa game da kalamai na baya bayan nan da Amurka ta furta da kuma abubuwan da ta aikata waɗanda sun ci karo da manufofin da ake son cimmawa ƙarƙashin yarjejeniyoyin ƙasashen biyu.

Blinken ya bayyanawa ɓangaren ƙasar Sin ra’ayoyin Amurka, da matsayarta, game da halin da ake ciki a Ukraine. Wang ya ce, abubuwan dake faruwa kan batun Ukraine, wasu batutuwa ne da ƙasar Sin bata son ganin faruwar hakan.

Batun Ukraine al’amari ne mai sarƙaƙiya, wanda ba kawai ya shafi haƙiƙanin manufofin ƙasa da ƙasa bane, har ma ya shafi bukatun tsaron ɓangarori daban-daban, a cewar Wang, inda ya buƙaci a mayar da hankali, ba kawai kan batun warware rikicin dake faruwa a halin yanzu ba, har ma da tabbatar da samun ɗorewar zaman lafiyar shiyyar baki ɗaya.

Fassarawa: Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *