Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed da takwaranta a ma’aikatar noma, Mahmud Muhammad Abubakar sun sha kaye a rumfunan zaɓensu a hannun ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
Ministocin ‘yan asalin Jihar Kaduna ne kuma a halin yanzu suna cikin Majalisar Ministocin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Ministar Kuɗi, Hajiya Zainab Ahmed ta sha kashi a rumfar zaɓenta mai lamba 053 a Kawo, Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, inda a zaɓen Shugaban Ƙasa APC ta samu ƙuri’u 8, NNPP 5, Jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 15.
Ministan Noma, Mahmud Muhammad Abubakar ya sha kaye a rumfarsa ta Tudun Wada, inda PDP ta samu 92, APC 66, Labour Party 1.