Mun daƙile hari a Kano da ka iya zama mafi muni a Nijeriya – Janar Irabor

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Babban Hafsan tsaro na Nijeriya, Janar Lucky Irabor, ya ce dakarun soji sun daƙile wani yunƙurin kai hari a Jihar Kano, “wanda ka iya zama mafi muni a tarihin ƙasar nan.”

Janar Irabor ya bayyana hakan ne a Lahadin da ta gabata, ya yin wani shiri na neman ’yan Nijeriya su ci gaba da kyautata zato ga ƙasar nan a yayin bikin ranar Dimokuraɗiyya da kafar talabijin ta Channels da dauki nauyi.

Ya ce an daƙile harin ne a Kano cikin makon da ya gabata, an kai hari kan wani cocin Katolika a garin Owo na Jihar Ondo, wanda ’yan bindiga suka buɗe wa masu ibada wuta.

Rahotanni sun nuna   cewa, aƙalla mutum 40 ne aka tabbatar da sun rasu a yayin harin da aka kai, inda sama da mutum 120 kuma suka samu raunuka yayin harin da aka kai a Cocin St. Francis Catholic a garin Owo a ranar Lahadi, 5 ga watan Yunin 2022.

Gwamnatin Tarayya ta ce ’yan ta’addan ƙungiyar ISWAP ne suka kai hari kan Cocin a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola da yake magana da manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa jim kadan bayan kammala taron Majalisar Tsaro ta Ƙasa a ranar Alhamis ta makon jiya.

Da ya ke magana dangane da harin na Owo, Janar Irabor ya ce, “Babu mamaki ba ku da labari cewa a makon da ya wuce kaɗai da aka kai harin Coci a Owo, a Kano misali, mun yi nasarar daƙile harin da ka iya zama mafi muni a tarihin ƙasar nan tamu saboda bayanan sirri da muka samu,”

“A wannan aikin, mun gano kayayyakin da ake haɗa abubuwan fashewa da su,” inji Irabo

Kazalika Janar Irabor ya ce sun kwace ƙunshin makamai masu yawan gaske da miyagu ke ƙoƙarin yin amfani da su a sassan ƙasar nan ciki har da Abuja.

Sannan ya karkace da cewa harin Owo da aka kai ba ya nuna cewa ba a samun ci gaba a faɗin Nijeriya ba, yana mai cewa “harkokin tsaro sun inganta a shekara ɗaya da ta wuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *