MURIC ta buƙaci a gaggauta yin adalci kan kisan Sheikh Aisami

Daga BASHIR ISAH

Ƙungiyar Kare ‘Yancin Musulmi (MURIC) ta yi kira da a gaggauta yin adalci kan kisan shahararren malamin nan Shaykh Goni Aisami da wasu sojoji biyu suka yi.

MURIC ta bayyana kashe malamin da aka yi a ranar Juma’a, 19 ga Agustan 2022 a matsayin kisan wulaƙanci wanda ya zama wajibi a bi wa marigayin kadinsa.

Ƙungiyar ta yi waɗannan kalaman ne cikin sanarwar manema labarai da ta fitar ran Litinin ta hannun daraktanta, Farfesa Ishaq Akintola.

Sanarwar ta ce, “Wani soja da ya yi iƙirarin yana bakin aiki ya kashe fitaccen malamin Islaman nan da ke Gashua, Jihar Yobe, Shaykh Goni Aisami a ranar Juma’a, 19 ga Agusta, 2022 bayan da sojan ya baƙaci malamin ya rage masa hanya daga Nguru zuwa Jajimaji.

“A hanyarsu ta tafiya ne sai sojan ya umarci malamin ya tsayar da motar, inda ya harbe shi sau uku sannan ya yar da gawarsa.

“Daga nan sojan ya kira wani abokin aikinsa kan ya zo ya taimaka masa saboda motar ta ƙi tashi. Kuma dukkan ƙoƙarin da suka yi don tayar da motar hakan ya ci tura, har sai da mazauna yankin suka gano gawar malamin da kuma yadda sojojin ke ta fama da motar, wanda hakan ya sa suka gaggauta sanar da ‘yan sanda.

“Yayin da muka yaba da ƙoƙarin Rundunar ‘Yan Sandan Yobe wajen cafke waɗanda ake zargi, haka ma muna kira da a gaggauta yin adalci kan kisan wulaƙancin da aka yi wa malamin.

“Dole a gurfanar da sojojin a kotu da zarar ‘yan sanda sun kammala bincikensu. Muna gargaɗin kada a yi kumbiya-kumbiya cikin lamarin,” inji MURIC

Ƙungiyar ta ce sojojin da lamarin ya shafa mugun iri ne a cikin sojojin Nijeriya waɗanda suke janyo ɓacin suna ga takwarorinsu.

Ta kuma buƙaci a zurfafa bincike mai yiwuwa a sake gano wasu ɓatagari daga cikin sojojin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *