Na fitar da littafin ‘Gaba Gaɗi’ ne don na shirya dawowa gaba-gaɗi – Jamila JUT

“Abin da ya sa na sauya salon rubutu”

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

A daidai lokacin da ake ganin kasuwar littattafan Hausa ta gama mutuwa wadda har ta kai marubuta da dama an daina ganin littattafansu, sai ga shi wasu daga cikin fitattun Marubutan da a ke ganin kamar sun ajiye alƙalamin su sun fara dawowa harkar da wani sabon salo na rubuta littafin. Jamila Umar Tanko, wanda aka fi sani da JUT, a nata salo na tafiya da zamani, ta zo da salon da za ta ci gaba da rubutun ta yadda masu karatu za su rinqa samu su karanta a duk lokacin da suke buƙata. Ko wanne irin salo ne? Wakilinmu ya tattauna da ita. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance:

MANHAJA: Ki na daga cikin marubutan da suka yi fice a harkar rubutun littattafai tsawon shekaru da su ka gabata, wanda a yanzu zamani ya sa da yawa daga cikin ku an daina ganin rubutun ku, sakamakon harkar da ta sauya salo, ko a wane hali harkar rubutu take a wannan lokacin? 
JUT: To gaskiya ne, mu ne dai tsofaffin Marubuta, mun ga jiya, kuma ga shi Allah ya kawo mu wannan lokacin. A baya littafi kafin mu fitar a na zaman jiran mu ne, kuma daga mun fitar da littafin sai ka ga an zo daga gari gari an cika buhu-buhu an tafi da su, to a wannan an ci gajiyar rubutun sosai. To kuma daga baya, idan ka fitar da littafin sai ka ga mutum ɗaya ya ɗauka ya je ya rubuce shi a shafin ‘Facebook’, wannan ya jawo aka samu ƙarancin masu karatun littafi, don karatun ya koma sai a waya. 

To, da mu ka ga haka ne sai muka koma gefe don kusan duk littattafanmu an ɗauke an rubuce shi a ‘Facebook’, ya zama ba mallakar mu ba, an miƙa su a ‘Social Media’, duk masu karatu babu ruwan su da su je kasuwa su saya tun da su na da shi a waya. To saboda haka ni dai a nawa vangaren sai na dakata, duk da cewar ina da labarai masu yawa, amma dai a haka na haqura, don ba zan yi rubutun da Ina ji ina gani za a saka mini ciwon zuciya ba, ni na rubuta, amma ya zama ba nawa ba, ka yi magana kuma a zage ka, don haka a yanzu rabon da na yi rubutun littafi a yanzu shekaru biyar kenan. Kuma ban tava sha’awar cewar zan dawo rubutu ba, sai ya zama ‘yan kasuwa da masu karatun littattafai na su ka yi ta yi mini maganar ya kamata na rinƙa yin rubutun a yanzu, don akwai tsarin fitar da rubutun da a ke yi, akwai Marubuciya Sumayya da a yanzu ta ke yin littafi bisa wani sabon salo, kuma ita ma ta na yi ne ko za ta ci riba ko ba za ta ci ba, tana fitar da shi kawai, kuma sai suka tabbatar mini da cewar ana sayen littafin sosai, kuma tun da mu a na son littafinmu idan mun yi za a saya, to sun dai ɗauki lokaci su na faɗa mini, amma dai ban yarda ba.

To, kamar wasa a ‘yan kwanakin nan, da ma akwai littafin da na ke da shi wanda ban sake shi ba, na dai yi tallan sa dai a baya kawai ban sake shi ba ne, don ban san yadda zan saki littafin kuɗin sa ya dawo ba. To, sai Sumayya Takori ta ba ni shawara cewar a yanzu an sauya salo ko ta ‘WhatsApp’ ma za ka iya sayar da littafin kuma ga ‘YouTube’, ga ‘Okada’. Sai a wannan watan na Satumba da ya wuce, Nura Sada Nasimat ya yi mini magana cewa kasuwar ‘online’ ta na tafiya a yanzu, ya kamata na shigo a yi da ni domin idan muka shigo, to kowa zai zo a yi da shi. Kuma akwai wani bugun littafi da a ke yi a yanzu kai tsaye daga ‘Computer’ babu wani kashe kuɗi da a ke yi ko da kwafi biyu ki ke so a ranar za ki same shi. Da na samu gamsuwa da maganar sa sai na fara wanda a yanzu na fitar da littafin na farko, kuma ko da na fara abin kamar wasa, ashe masu karatu na su na can su na jira na don haka a ranar da na fara na bayar da lambar waya ta da Asusun ajiya ta na Banki, na saka a kan Naira 500 duk wanda zai karanta a ‘online’, sai a ka yi ta shiga ‘Group’ ɗin na ga a na ta turo mini kuɗi. Kuma kai tsaye na ke rubuta littafin na tura musu. To ban tava yin littafin da na gama kashi na ɗaya a kwana goma ba sai wannan.

Amma idan da aka samu matsala, na yi kashi na tara, kawai sai aka samu wata daga cikin ‘group’ ɗin ta fitar da shi, duk da cewar doka ce sai an faɗa wa kowa cewar Amana kada wani ya fitar da littafin zuwa wani ‘group’ ɗin, kuma duk sun yi alƙawari za su goya mini baya, amma kawai na kammala na takwas zan shiga na tara, sai kawai aka ga tun daga na ɗaya zuwa na takwas ɗin an kwashe an kai shi wani ‘group’ ɗin, har a na tambayar ba ni shafi kaza wasu ma su na ta cin kasuwar sa. 

To, sai aka ɗauko mini tare da sunan wadda a ke zargin ita ce ta fitar. Amma da na tambaye ta sai ta ce ita ma a gari ta tsinta. Na ke ta bin didigi a cikin ‘group’ ɗin wace ce ta ɗauka ta fitar da shi, aka nema aka rasa kowa ta ce ba ita ba ce. Daga nan aka ce na yi haƙuri an ja musu kunne na ci gaba, sai na saki kashi na tara. Ai kuwa ina sakin sa kafin na kwanta bacci a daren har an ɗauke shi an yaɗa shi. Sai na yi rubutu na ce to daƙiƙiyar cikin mu ta sake ɗauka, kuma na ce ko wace ce ta sanar da ni ba zan tona mata asiri ba, amma ta ƙi yin magana, kuma ga shi na turo wani ta sake ɗauka, don haka na haƙura da rubutun, waɗanda su ka biya kuɗin su, sai su yi mini magana na mayar musu da kuɗinsu. 

Sai ya zama maganar da na yi na daƙiƙiyar cikinmu bai kamata na yi wannan maganar ba, wai a matsayi na na babbar marubuciya bai kamata na yi wannan maganar ba. Wannan ya sa na kasa gane rashin adalcin da a ke yi wa Marubuta, su a tunanin su dole na saki rubutun, su karanta. Har ma wasu su ke cewa, idan ma ba za ta yi ba, daga ina ta tsaya na ci gaba, duk aka rinqa faɗar haka a cikin ‘group’ ɗin, wannan ta sa na ja na tsaya daga kashi na tara. Sai na ga a she yawan sa ma ya kai na fitar da littafi shafi 160 daidai yadda za a buga, saboda haka sai na tura aka buga mini, sai ya ce kada na buga da yawa sai an samu waɗanda aka san za su saya idan sun turo da kuɗin sai a buga musu. Yanzu dai na ce a buga mini guda 50 na gani.
Amma na ‘online’ dai su na nan su na jira na, saboda sun biya ni kuɗi, ni kuma na kasa sakar musu, saboda ita wadda ta ke kwashe rubutun ta na nan ta na jira na saka ta kwashe. Don haka ni dai gaskiya ban ga kasuwa a wannan na ‘WhatsApp’ ba. Amma dai yanzu shawarar da aka ba ni na sake buɗe wani ‘group’ ɗin a samu mutum ɗari biyu da suka biya sai a rinƙa yin kasuwancin da su. Don yadda na fara da mutum ɗaya biyu uku daga nan na samu matsala, amma Idan aka ce fita dole ya fita, idan na tara masu karatun shi ne zai zama ko da ya fita ɗin to na samu abin da na samu. Ina ganin shi ne abin da zan yi a nan gaba. 

To, a ɓangaren ‘YouTube’ kuma ta ina ku ke samun kuɗi? 
Eh, gaskiya kafin na saka shi a ‘WhatsApp’ daman sai na saka shi a ‘YouTube’, Don na samu wanda ya ke karantawa ina ɗora shi, kuma shi ‘YouTube’ gaskiya ya fi zama idan har ya karɓu, don shi akwai adadin mutanen da za ka tara sannan su fara biyan ka, don haka sabo na buɗe Jamila Umar Tanko Chanal, yanzu na fara ba a fara biya na ba, amma dai kullum ina ƙara samun masu bibiyar shafin kuma ina tunanin shi ne ma hanya da zan tsaya da ƙafa ta sosai, wanda babu wanda ya isa ya satar mini littafin, kuma kafin na saka a ‘YouTube’ zan fara buga shi ina fatan idan aka gane shi sosai ‘YouTube’ za su fara biya na. 

To, shi wanda ki ka fara na kai tsaye daga kwanfuta fa? 
Eh, shi wannan gaskiya har mutane sun fara ajiyar kuɗin su, kuma shi ya na da tsada, don za a sayar da shi ne a kan naira 1000 kwafi ɗaya, amma dai an ce mutane su na saye a hakan. 

Amma yanzu wannan littafin idan mutum ya na son kwafi zai saya, kuma ya na Sakkwato ko Abuja, ta ya za a yi ya saya? 
Eh, gaskiya mun fi magana da masu sari, don ka ga a yanzu wata ta yi mini magana ta na son kwafi goma, kuma duk a na kira na daga garuruwa ana son a saya a hakan. Kuma a cikin waɗanda su ka saya su na karantawa ta ‘WhatsApp’ na ce su cika kuɗin sai a ba su kwafin littafin tun da a yanzu na dakatar da na ‘WhatsApp’ ɗin, don mutane da yawa sun fi son littafin a yanzu. 

To yanzu haka zan koma kuma ina da tunanin na dawo da tsofaffin littattafai na cikin wannan tsarin. Amma dai a yanzu abin da na fahimta, martabar littafin ce ta dawo, domin wanda a ke sayen sa a naira 120 a baya, yanzu ya koma 1000, kuma na ji an ce Bilkisu Salisu Funtua ita ma ta dawo da kusan duk littattafan ta a na sayar da su. Don haka tun da ina son na ci gaba da rubutun dole sai na bi hanyar da zamani ya zo da ita. Amma dai ni abin zai fi mini sauƙi a yanzu, saboda wahalar da mu ke sha wajen sayo takarda tun ma ba ta kai hakan ba, ga sauran ayyukan da su ke gaba, to saboda haka ina ganin kai tsaye daga ‘Computer’ ɗin zai fi sauqi a wajen mu. A yanzu dai nawa ɗin ya fara fitowa mai suna ‘Gaba Gadi’. 

A yanzu wane irin shiri ki ka yi na tsara kasuwancin ki na nan gaba? 
To, gaskiya sabon tsari ne, kuma ina ganin in ba wani ikon Allah ba, ba za mu samu ribar littafi kamar yadda mu ka samu a baya ba, don ka ga za mu iya kashe kuɗi mu yi littafi, mu kai kasuwa, a kwana biyu ma ya ƙarribare, kuma ka samu kuɗi mai yawa, amma a yanzu sai ka zauna zaman jira, ko a ‘YouTube’ ɗin ko a ‘WhatsApp’ ɗin ni dai da na zauna na yi lissafin sai na ga ko da za mu samu riba to ba za ta kai irin wadda mu ke samu a baya ba. 
Kuma abin da ya fi ba ni mamaki da takaici shi ne, wannan kasuwar ta ‘WhatsApp’, cike take da qananan yara, kowa zai iya faɗa maka magana, savanin a baya, sai a neme ka a waya a gaishe ka, a mutunta ka, amma a yanzu idan ku na magana a ‘WhatsApp’ za ta iya zagin ka. To wannan ta sa ina saka kai sai na yi baya, to amma dai a haka dai za a yi gwagwarmayar, don haka zan ci gaba da na ‘WhatsApp’ ɗin a kan sabon tsarin da zan fitar, duk da an ce ya na da ƙarancin tsaro, don haka idan ka duba a baya su marubutan da shi kan sa rubutun a baya sun fi ƙima da daraja. Don ka ga tun farko da suka fara ɗaukar littafin mu su na sakawa, da ni da Fauziyya D. Sulaiman da Sadiya Garba mu ka shiga muna magana, sai ka ji zagi, amma idan ka duba, sai ka ga yaron ɗan shekaru 15 ne ɗan cikin ka ne, ya na cewa, ai kasuwa su ka je, su ka sa kuɗin su su ka saya, don haka su na da damar da za su yi tun da kuɗi su ka biya, kuma ko a yanzu ma haka su ke faɗa, kuma babu yadda za ka fahimtar da su, saboda ba su da ilimi. Wani kuma namiji ne ya yi sunan mace ya sa maman wance, to gaskiya akwai matsala a cikin rubutun Soshiyal Midiya, saboda babu mutunci kamar na da.

Bangon littafin Gabs Gaɗi

Kuma sai ya zama ban sani ba marubutan ‘Online’ su na da yawa da ƙungiyoyi masu yawa, sai su ka yi mini ca! Su na yi mini sannu da zuwa, su na murna manyan marubuta sun dawo ‘online’, ni ban sani ba sai suka fara yi mini tallan ƙungiyoyin su, wai akwai ƙungiyar da idan ka yi rubutu a na yi maka gyara. To sai na ga idan har ban gyara musu ba, ai ba za su ce za su gyara mini ba. Haka dai su ka yi ta kira na, su na faɗa mini sunan su, ni ban san su ba, a she ma sun yi suna a ‘online’ ɗin ne, har ma su na cewa su na da taro na je wajen taron. Kawai dai ina ba su haquri ne, ina cewa yanzu na shigo ku ɗan ba ni lokaci. 

Sai dai ni abin da na ji daɗin sa, duk littattafai na na baya da na duba a ‘YouTube’ gaba ɗaya an karanta su, don a yanzu babu wanda za a saka a shafina kuma babu yadda na iya kuma an ɗauka ba tare da sani na ba. To amma sabon littafin da zan yi nan gaba, kafin na saki sai na saka shi a shafina, don haka babu in da za a same shi sai a waje na, ina fatan za a rinqa bibiyar shafi na wanda ta hakan ne za a ba ni ƙarfin gwiwar ci gaba da rubutun. 

Ko mene ne saqonki na ƙarshe? 
Saƙo na na ƙarshe, in dai Marubuta irin na baya su ka sake fitowa, kuma mu ka ƙara inganta abin, wasu sababin tunani su ka ƙaru, to gaskiya za mu ci ribar abin, don haka sai mu yunƙuro mu tafi da zamani, domin mu na da labarai masu yawa, mun ajiye su saboda yanayin kasuwar, mu ka bari don yanzu wasu Marubuta da yawa sun sauya sana’a. To amma dai bai kamata a bar harkar rubutun ba gaskiya, don a yanzu da na shigo na ga abubuwan da su ka zame mini darasi. Don kuwa Duniyar Online ban sani ba a she duniya ce ta masu karatu miliyoyi daga ƙasashe daban-daban, har ma sun fi na lokacin baya yawa, kuma har yanzu ba a manta da mu ba, don ga sabbin Marubuta nan, amma a na cewa na dawo sai mutane su ka rinqa rubibi na. Saboda haka sabon littafin da na fitar a yanzu mai suna ‘Gaba gaɗi”, to na shigo ne Gaba gadi, shi ya sa ma na ba shi wannan sunan. Don in sanar da masoyana na fito gaba gaɗi. Don haka na shigo kuma na ga kura-kuran da na yi zan gyara nan gaba, ina nan tare da manyan labarai na wanda zan rinƙa fitar da su nan gaba, kuma ina godiya ta musamman ga Khaleesat Haiydar da Alresha bisa gudummawar da su ka ba ni wajen qarfafa mini gwiwa a kan wannan dawowar da na yi. ina fatan Allah ya yi mana jagora. 

To, madalla mun gode. 
Ni ma na gode sosai.