Nijeriya ta ƙetare iyaka a cin bashi, cewar Ofishin Kasafin Kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Shugaban Kasafin Kuɗi na Tarayya, Ben Akabueze ya koka kan shirin karɓar rancen Nijeriya, inda ya ce, al’ummar ƙasar na iya shiga matsala.

Akabueze ya yi wannan jawabi ne ranar Laraba a wajen taron ƙaddamar da sabbin zaɓaɓɓun ’yan majalisar wakilai na ƙasa karo na 10, a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa (ICC) da ke Abuja.

Damuwa da fargabar nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya miƙa sabon buaatar neman lamunin dala miliyan 800 ga Majalisar Dokokin ƙasar domin biyan buaatun matsugunan gidaje miliyan 10.2 akan naira 5,000 kowanne.

Shugaban ya ce, rancen, a matsayin wani ɓangare na shirin shiga tsakani na gwamnati, zai dagula ayyukan yau da kullum kamar; inganta abinci mai gina jiki, kiwon lafiya, ilimi da cigaban jarin ɗan Adam na gidaje.

Da yake jawabi a wajen qaddamar da zaɓaɓɓun ’yan majalisar, Mista Akabueze ya ce ƙasar nan na ɗaya daga cikin aasashe mafi ƙarancin cigaba domin yawan basussuka a duniya.

Akabueze ya kuma soki tsarin kasafin kuɗin ƙasar, yana mai cewa Nijeriya ba ta da dokar Kasafi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *