Nijeriya ta kwaso ‘ya’yanta 167 da suka maƙale a Libiya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Sha’anin Masu Hijira ta Ƙasa-da-ƙasa (IOM) sun dawo da ƙarin ‘yan Nijeriya su 167 daga ƙasar Libiya waɗanda suka maƙale a ƙasa bayan da aka yi safararsu don ayyukan aikatau.

Malam Kabiru Musa wanda shi ne mai sanya ido kan shirin Nijeriya a Libiya, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Talata a Abuja.

Musa ya ce ‘yan Nijeriyar su 167, sun baro babban filin jirgin saman Mitiga da ke Tripoli ran Talata da daddare inda suka iso babban filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a jiya Laraba.

Ya ce Gwamnatin Tarayya ta bada dama ta musammam ga IOM da kuma shirin Nijeriya a Tripoli ne sakamakon ganin yadda dubban ‘yan Nijeriya suka maƙale a ƙasar.

Ya ci gaba da cewa wannan shiri shi ne irinsa na farko a wannan shekarar wanda ya shafi mutanen aka yi safararsu da waɗanda ake kaiwa aikatau bisa tilas da waɗanda aka sake su bayan an tsare su ba a bisa ƙa’ida ba da sauransu.

Jami’in ya ce tuni sun riga sun kammala dukkan tsare-tsaren da ake buƙata don sadar da waɗanda aka dawo da su ɗin da iyalansu.

Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da mata da maza har da ƙananan yara.

Libiya ta saba ganin ‘yan Nijeriya masu maƙalewa a cikinta kasancewar ta nan masu ƙoƙarin ƙetarawa zuwa sassan duniya daga Nijeriya kan bi don cimma buƙatunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *