Daga UMAR M. GOMBE
Majalisar Tarayya ta amince da kasafin Naira bilyan N4.87 da aka ware don amfanin Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa (NIA) wajen bibiyar kiraye-kiraye da saƙonni a wayoyi haɗa da Thuraya da manhajar WhatsApp.
Kuɗaɗen wani ɓangare ne na ƙarin kasafin Naira biliyan N895.8 da Shugaba Buhari ya nema a watan jiya wanda Majalisar Dattawa da ta wakilai suka amince da shi a makon jiya bayan da suka cilla kasafin da ƙarin biliyan N87.
A cewar Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Rabon Kasafi, Sanata Barau Jibrin, za a yi amfani da ƙarin kasafin ne wajen samar wa sojoji ƙarin kayan aiki da kuma ƙarfafa sha’anin yaƙi da cutar korona.
Bayanan da Manhaja ta samu dangane da kasafin sun nuna Hukumar NIA za ta samu kason N2,938,650,000 wanda za ta yi amfani fa shi wajen bibiyar Thuraya, sannan kason N1, 931,700,000 wajen leƙen asirin WhatsApp.
Kazalika, Hukumar NIA ta samu ƙarin milyan N129 don ba ta damar ɗaukar nauyin jami’anta zuwa samun horo a ƙetare.
Daga cikin kasafin, hukumar tsaro ta Defence Intelligence Agency, ta samu kason bilyan N16.8b wanda ake buƙatar ta yi amfani da kuɗaɗen wajen samar da kayan aiki, gina cibiyar tattara bayanan sirri da ɗakin bincike da sauransu.
Daga cikin kason Naira bilyan 33.6 da Ma’aikatar ‘Yan Sanda ta Tarayya ta samu, an ware milyan N200 don yi wa cibiyoyin bada horo guda 19 da ma’aikatar ke da su a faɗin ƙasa. Yayin da aka ware bilyan N4.1 don ciyar da masu karɓar horo, an kuma sake ware milyan N910 don biyan su alawus da dai sauransu.