PDP ta zargi Matawalle da tilasta wa jami’an INEC ƙara ƙuri’un jabu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara na zargin Gwamna Bello Matawalle na shirin yin maguɗin zaɓe na sahihancin sakamakon zaɓen mahaifarsa Ƙaramar Hukumar Maradun.

Jam’iyyar PDP a wata sanarwa da ofishin yaɗa labarai na Dauda Lawal ta fitar, ta ce, gwamnan ya tuntuɓi manyan jami’an INEC a ƙoƙarinsa na ganin an bayyana sakamakon zaɓen.

Ta kuma yi zargin cewa gwamnan, ɗan jam’iyyar APC, ba ya son amincewa da shan kaye cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *