Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Real Madrid, Florentino Perez, ya harbu da cutar korona.
Ƙugiyar Madrid da kanta ta sanar da hakan a shafinta na ‘Twitter’ a Talatar da ta gabata.
Inda ta ce, “Real Madrid CF na sanar da cewa an gano shugabanmu Florentino Perez ya kamu da cutar korona bayan gwaje-gwajen da aka yi masa, duk da dai bai nuna wata alamar kamuwa da cutar ba.”
Da wannan, ana sa ran Perez ya shafe sama da mako guda a killace har sai an tabbatar ya rabu da cutar kafin ya koma bakin aiki a Santiago Bernabeu.