Rashin shugabannni masu kishin al’ummarsu ne babban ƙalubalenmu – Hajiya Zulaihat Abdullahi

“Rayuwar mace a siyasa na da haɗari sosai”

“Addu’ar mijina ce ta sa nake ganin nasara a siyasata”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Dimukraɗiyya tsari ne da yake bai wa kowanne ɗan ƙasa ýanci ya zaɓi shugaban da yake so ya jagoranci al’amarin ƙasar sa ko yankinsa, haka kuma yana da ýancin shiga takara don neman goyon bayan jama’a shi ma a zave shi. Shi ya sa jama’a ke murna da zuwan lokacin zave, domin kowa ya shiga a dama da shi. Sai dai ba kasafai tsarin dimukraɗiyya da yanayin gudanar da siyasa musamman a yankin Arewa yake bai wa mata damar su ma su shiga a dama da su kamar sauran maza ba. Shi ya sa mata ƙalilan ne ake gani suna taka rawar gani a harkokin siyasa, babu ma kamar wannan kakar siyasar da mata da yawa suka zama ýan kallo, duk kuwa da kasancewar su ne suka fi ba da gudunmawa a wajen zave. Wata mace mai kamar maza da ta sha bamban da sauran mata ýan siyasa ita ce, Hajiya Zulaihat Aliyu, ýar gwagwarmaya, ýar siyasa kuma malamar makaranta, wacce yanzu haka take mara wa ɗan takarar Gwamnan Jihar Filato a ƙarƙashin Jam’iyyar APM baya a matsayin mataimakiya, daga ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a shiyyar arewacin Filato. Wakilin Blueprint Manhaja a Jos, Abba Abubakar Yakubu ya zanta da wannan jajirtacciyar ýar gwagwarmaya da ta ce burinta a siyasa shi ne, ta ga ta inganta rayuwar mata da matasa.

MANHAJA: Ki gabatar mana da kan ki.
ZULAIHAT: Sunana Hajiya Zulaihatu Aliyu Abdullahi. Sunan mahaifina, Alhaji Ali Abdullahi, wanda aka fi sani da Alhaji Ali Dogo, Allah Ya jikan sa da rahama. Ni ýar siyasa ce mai kishin kawo canji a rayuwar mata da matasa. Ni uwa ce, Ina da aure da yara 5. Sannan kuma ni ýar kasuwa ce, don Ina harkokin saye da sayarwa, Ina kuma harkar koyarwa.

Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki a taƙaice?
Alhamdulillah. Ni dai na tashi ne a babban gida, mai iyali da yawa, don haka rayuwa a wajena gwagwarmaya ce da neman abin dogaro da rufin asiri. Na yi karatun firamare makarantar firamare ta Baptist a unguwar Nasarawa cikin garin Jos, Na yi sakandire har wa yau a ɓangaren Baptist Academy , har zuwa aji uku na qaramar sakandire.

Sai na koma karatu makarantar nazarin ilimin addinin Musulunci ta School for Higher Islamic Studies da ke titin Sarkin Mangu ƙarƙashin kulawar ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah, a nan na samu shaidar koyarwa ta Grade 2. Daga nan na ci gaba da neman ilimin koyarwa a Kwalejin Malanta ta ƙasa NTI, inda na samu shaidar koyarwa ta N.C.E.

Sannan na samu digirina na farko a Jami’ar Jos, inda na karanta yadda za a koyar da ilimin zamantakewar ɗan Adam. A duk tsawon waɗannan shekaru rayuwata ta shagala ne da neman ilimi, koyarwa da kuma kula da iyalina.

Wacce gwagwarmaya ki ka sha a rayuwa da ta mayar da ta inganta rayuwarki, zuwa matsayin da ki ke ciki?
To, kamar dai yadda na fada a baya akasarin rayuwata ta tafi ne wajen neman ilimi da koyar da shi. Na ɗauki tsawon shekaru goma sha huɗu Ina koyarwa. Na koyar a makarantu har guda uku, wanda hakan ya koya min abubuwa da dama na sha’anin rayuwa da zaman tare.

Kasancewar mun rayu a lokacin zamantakewar al’ummar Jihar Filato na cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali, bayan da aka samu savani na rikice rikice, na samu kaina cikin mata ƙalilan da suka haɗa kai da matasa wajen gwagwarmayar samar da zaman lafiya da yaƙi da shaye shaye da amfani da makamai wajen faɗace faɗacen daba a tsakanin matasa, sakamakon tasirin rayuwa cikin rikice rikice. Wannan ya ƙara gogar da ni wajen sanin muhimmancin zaman lafiya da rungumar kowanne mutum ba tare da nuna wariya ko bambanci ba.

Ba ni labarin yadda ki ka fara siyasa?
Gaskiya ni dai a baya bani da niyyar shiga siyasa, amma shiga ta harkar gwagwarmayar kare ýancin mata da haƙƙoƙin raunana na fahimci muhimmancin idan aka samu shugabanci nagari abubuwa da yawa za su sauya.

Amma qalubalen da muke fuskanta wani lokaci shi ne, rashin shugabannni masu kishin al’ummarsu, waɗanda suka san damuwar jama’a kuma suke da burin ganin sun inganta rayuwarsu da muhallin da suke rayuwa a ciki. Don haka na nemi izinin maigidana kan cewa, Ina son in shiga in ba da gudunmawata a harkar siyasa tun da yanzu na san jama’a, kuma na fahimci yadda al’amuran suke tafiya.

Ban samu matsalar shawo kansa ba kuwa ya fahimce ni, kuma ya ba ni goyon baya. Dama shi mijina mutum ne mai sauƙin kai, kuma wayayye da yake da kishin cigaban rayuwar mata, musamman ma kuma ni da a ko da yaushe yake alfahari da nasarorin da nake samu. Tun da ya sa min albarka, kuma na je na sanar da iyayena su ma suka albarkaci wannan kyakkyawar niyya tawa, sai cigaba nake samu har kawo yanzu.

Na fara da bin ýan siyasar da ra’ayin siyasar su ya zo daidai da nawa, daga bisani kuma har na zama shugabar Jam’iyyar NUP, kafin daga bisani bayan Babban Zaven 2015 Hukumar Zave ta INEC ta soke rijistar jam’iyyar da ta wasu jam’iyyun da ba mu samu cin kujeru a zave ba. Wannan ya sa na koma jam’iyya mai mulki ta APC, amma nan ma fahimci tsarin su ba irin wanda nake so na gina siyasata a kai ba ne.

Don haka na koma jam’iyyata ta APM, yanzu kuma nake takarar mataimakiyar gwamna tare da jagoran takarata kuma gogaggen ɗan siyasa, Alhaji Muhammad Abdullahi Ɗanbaba.

Wanne darasi ki ka koya a harkar siyasa kawo yanzu?
A gaskiya na koyi darasi da dama a harkar siyasa. Na farko na koyi shiga cikin jama’a ba tare da jin tsoro ba ko shakka. Na koyi magana a cikin jama’a, duk yawansu ba ya razana ni, kuma zan yi magana ba tare da rawar jiki ba. Zan isar da saƙon da nake son isarwa. Na kuma lura cewa su ‘yan siyasa duk wadatarsu ba sa so ka zama mai zama kullum kana roƙon su ko kuma ka riqa jiran su ɗauko su baka.

Yana da kyau wata rana kai ma ka yi ƙoƙari ka musu wani abin da za su ji daɗi. Misali ka buga jaka, littattafai, robobin ruwan sha, riguna da hulunan masu yaƙin neman zaɓe da sauransu, kai ma ka ba su kyauta a matsayin gudunmawar ka. Sannan kamun kai musamman ga ‘ya mace, saboda kuwa rayuwar ýa mace a siyasa tana da haɗari sosai. Idan mace ta fara siyasa ba kamun kai to, wallahi ba inda za ta je.

A haka za ta gama ba ta san inda ta dosa ba. Amma idan ta riƙe mutuncin ta, ba sai ta fito ta nema ba, tana zaune za a neme ta da matsayi ko wani abin alheri a bata.

Yaya ki ka samu kan ki a matsayin mataimakiyar ɗan takarar Gwamnan Jihar Filato a Jam’iyyar APM?
To, Alhamdulillah. A gaskiya ban fuskanci wata matsala ba. Kamar yadda a baya na gaya maka halin mutum jarinsa. Zaman da na yi da sauran ýan siyasa da shugabannin jam’iyyu ƙarƙashin Majalisar Haɗin Kan Jam’iyyu ta IPAC na samu gogewa da mu’amala da ýan siyasa.

Na zauna da kowa lafiya, musulmi da Kirista duk nawa ne, cikin biyayya da girmamawa, kuma wannan abin ne ya kawo ni ga wannan matsayin, inda shi ɗan takarar Gwamnan mu Alhaji Muhammadu ɗanbaba ya ga ya dace ya gayyace ni, domin in zama abokiyar takarar shi, bayan nasarar da ya samu a zaven fid da gwani, sakamakon yadda ya lura na bambanta da sauran matan a halayyata da ilimina.

Sannan da kuma dubawa da yayi ya ga ni mace ce mai jama’a kuma tafiyar mu tare zai janyo hankalin mata da dama su jefa mana ƙuri’unsu.

Wacce gudunmawa za ki bayar ga cigaban rayuwar mata da matasa, idan Jam’iyyarku ta samu nasara a Babban Zaɓen 2023?
Da izinin Allah idan har Jam’iyyarmu ta samu nasara zan yi iyaka ƙoƙari don in ga cewa ba a bar mata da matasa a baya ba. Duk wani abin da za a yi a Jihar Filato, mata za su samu kashi 45 cikin ɗari. Kuma matasa za su samu ayyukan da za su dogara da kansu ba tare da sun jira gwamnati ba.

Mata a gida za su samu tallafin da za su yi sana’o’in dogaro da kai. Ko da ba su fita ba, domin sune suke bada kuri’a a ruwa ko iska, sanyi ko tsananin zafi ba ya hana su fita su jefa ƙuri’unsu.

Shin kin gamsu da irin rawar da mata ke takawa a fagen siyasar Nijeriya?
Kwarai kuwa. Babu shakka mata yanzu suna taka rawar gani a gefen siyasa ba kamar a baya ba, inda ake ganin cewa duk macen da take harkokin siyasa ‘yar iska ce. Yanzu kai ya waye mata sun gane muhimmancin neman ýancin kansu, da qoqari kan ƙwatowa sauran ýan uwa mata haƙƙoƙinsu da maza ba sa mayar da hankali a kansu.

Kina ganin matan da suke riƙe da manyan muƙamai a ma’aikatu da hukumomin gwamnati suna wakiltar mata yadda ya kamata?
A gaskiya ana samun jajirtattun mata da ke ƙoƙarin fitar da mata a kunya a ɓangarori daban daban na ayyukan gwamnati. A cikin siyasa ne dai zan iya cewa har yanzu da sauran mu. Amma idan aka cigaba da ba mu dama da jawo mu cikin harkokin tafiyar da mulki wata rana za mu goge sosai.

Sau da dama ýan siyasa mata irin ki suna fuskantar tsangwama da kyara da iyali ko ýan uwa, yaya ki ke ji a naki ɓangaren?
Ai kamar yadda na faɗa a baya ne, mata ýan siyasa na fuskantar tsangwama da kyara. Saboda ganin yadda maza suka mamaye harkar, don haka ake tunanin shigar mace cikin siyasa kamar shiga harkar baɗala ne da rashin kamun kai.

Amma na gode wa Allah ni a nawa ɓangaren tun kafin in fara siyasa mijina da iyayena su ne suke bani ƙwarin gwiwa da wasu shawarwari. Shi ya sa nake samun cigaba a rayuwata, ‘ya’yana suma kullum cikin addu’a da fatan alheri suke. Mahaifina har Allah ya karɓi ransa yana min addu’a da sa albarka.

Shin kin yarda da cewa da ake yi mata ba sa bai wa ýan uwansu mata goyon baya, musamman idan aka zo batun zaɓe?
Akwai wannan don wannan. Amma a yanzu abubuwa suna sauyawa. Mata sun fara fahimtar muhimmancin haɗin kai da aiki tare don samun cigaban rayuwar su, da ƙwato haƙƙoƙin su. Sai dai kuma sha’anin rayuwa ba ka iya raba mutum da halin sa, wannan a ɗaiɗaiku kenan.

Amma mafi akasari mata yanzu sun gane kuskuren su na baya, kuma da yardar Allah a wannan Babban Zaɓen 2023 mai zuwa za a ga canji sosai.

Jihar Filato na da ƙarancin mata masu tsayawa takara ko shiga siyasa, wanne sauyi ki ke ganin za ki kawo a wannan yanayi?
Wannan matsala ba a nan Jihar Filato kaɗai ba ne, matsala ce ta ƙasa baki ɗaya. Muna fatan daga cikin canjin da muke sa ran gani a harkokin siyasar mu, za mu duba mu ga menene dalilin da ya sa ýan siyasa mata ke ɓoye kansu. Za mu zaƙulo su duk inda suke don mu yi aiki tare.

A Jihar Filato akwai cigaba sosai. Idan ka lura akwai mata biyu da aka fitar su yi takarar Mataimakin Gwamna a jam’iyyun daban daban, akwai a Jam’iyyar PDP da kuma namu na APM. Sai dai duk da haka akwai buƙatar qara ƙarfafa gwiwa. Kwanaki da na je Abuja na ga matan da suke siyasa na yi mamaki matuƙa, a raina na ce ashe a Filato akwai ƙarancin mata ýan siyasa.

Wanne ƙalubale ki ke fuskanta kawo yanzu a wannan takara da ku ke yi?
Gaskiya babban ƙalubalen da nake fuskanta shi ne matsalar rashin kuɗaɗen tafiyar da harkokin yaƙin neman zaɓe, domin idan mutum ya fito takara babu shakka duk ajiyarshi sai ta ƙare. Amma da yardar Allah muna samun tallafi da goyon baya, kuma Ina da ƙwarin gwiwar samun nasara, in sha Allah.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?
Hassada Ga Mai Rabo Taki, sai kuma Zakaran da Allah ya nufa da Cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi.

To, madalla. Na gode.
Ni ce da godiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *