Rubuta fim ɗin da zai amfanar da al’umma ne babban burina – Yusra Yusuf

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Yusra Yusuf Yunusa wadda aka fi sani da Yusra AGM matashiyar da ta yi fice a wajen rubuta labarin fim a masana’atar Kannywood. A tattaunawarta da wakilin Manhaja a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji tarihinta da kuma irin faɗi-tashin da ta yi har ta kai ana karbar rubutunta a Kannywood. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Muna son ki gabatar mana da kanki ga masu karatunmu?

YUSRAH YUSUF: Sunana Yusrah Yusuf Yunusa, wacce aka fi sani da Yusra AGM Bashir kamar yadda ake kira na.

Ko za ki ba mu taƙaitaccen tarihinka?

Nayi karatu a Mai Gadon Ƙaya Primary school, sannan na yi karatun addinina a wata islamiyya mai suna Madarasatul Tahazibul Auladinnabiyi. Baya ga haka, na ta fi makarantar gaba da firamare, wato secondary school a Ima college da ke Maiduguri. Sannan na yi Jameel chroma college of science and technology.

Ta yaya aka samu kai a Masana’atar Kannywood?

Na samu kaina a masana’antar Kannywood ta hanyar yin rubutun fim wanda hakan dama shi ne burina tun Ina qarama nake sha’awar yin rubutu.

Masana’atar fim tana da faɗi, ke a ina za a iya cewa kin fi ƙwarewa?

To, gaskiya na fi lwarewa a fannin rubutu, duba da cewa, tun asali shi ne abinda na fi so na yi a dukka vangarorin da ake da su a masana’antar ta finafinai. Rubutu ne abinda nake buri tun da daɗewa.

Tsakanin rututu da kuma ‘acting’ wanne ne ki ka fara yi?

A gaskiya rubutu da kuma waƙa na fara yi a lokaci ɗaya. Yadda suka haxu kuwa shi ne, na kan rubuta wala, kuma na rubuta fim, dukka a littafi.

Daga lokacin da ki ka shiga masana’atar Kannywood zuwa yanzu finafinai nawa ki ka rubuta?

Gaskiya suna da yawa da ban iya lissafin su dukka ba, wannan kuma ba abinda zan ce da hakan sai dai na ce Alhamdu lillahi. Duk da hakan zan iya tuna wasu kaɗan daga cikinsu, irin su, ‘Jalilah’, akwai kuma ‘Bunayya’, akwai ‘Lokaci’, ‘Ruɗani’, ‘Halacci’, da sauransu.

Daga lokacin da ki ka fara zuwa yanzu waɗanne irin nasarori za ki iya cewa kin samu?

Da farko dai zan fara da cewa Alhamdu lillah, domin na samu nasarori da yawa, tun daga lokacin da mutane suka yarda na iya har ake ɗauka a bani, na yi, wannan ma abin godiya ne kuma babbar nasara ce a gare ni.

Idan mun koma vangaren ƙalubale fa, ko akwai waɗanda ki ka ci karo da su?

Gaskiya na fuskanci ƙalubale a harkar fim, amma idan an yi duba da cewa, ita ma harkar fim kamar sauran harkokin rayuwa ta ke, za ka ci karo da ababe da dama kafin ka kai ga nasara, dole sai ka yi haƙuri kafin ka cimma gaci.

Wane ne saurayinki na farko?

(Dariya). Magana ta gaskiya ba zan iya tuna sauranyina na farko ba.

Ya batun aure fa?

Maganar aure kasan abu ne daga Allah. Shi aure lokaci ne, da aure da mutuwa ba a saka masu rana.

Wane ne maigadanki a Kannywood?

AGM Bashir shi ne maigana kuma kawuna ne, ya bani gudunmawa sosai wajen nuna min hanyar da ta dace na bi, sannan bazan manta da wanda shi ne jigo wajen tallafamin nasan yadda zan sarrafa labari idan zan yi, shi ne Nazir Alkanawi, wanda shi ma ya haɗani da abokinsa Jamil Chiroma.

Rubutun fim shi ne ginshiƙi ga tasirin kowane fim da za a yi. Idan ya yi kyau, fim zai yi kyau. Menene shawarar ki ga ‘yan’uwanki marubata finafinai wajen ganin an inganta labarin fim?

Shawarata ita ce, mu dage wajen rubuta abinda ya kamata, sannan muna buƙatar faɗaɗa tunani yayin da muka zo rubutu labari, sannan kada mu yi abu da iya tunaninmu, mu dinga dogon bincike kan jigon labarin da muke rubutu kansa, tare kuma jin ta bakin waɗanda abin ya danganta na daga cikin mutane. Kamar al’adu, addini ko matsalolin rayuwa da muke son karkata rubutun namu kansu. Ta hanyar yin hakan zai sa mu haifar da ingantaccen rubutu da zai bayar da fim mai ma’ana.

Menene burinki a masana’atar fim ta Kannywood?

Burina a ɓangaren fim shi ne, na amfanar da duk wanda yake cikin wannan masana’antar, ta yadda zai zama aikina ya yi tasiri a wannann masana’atar fim ta Kannywood. Babban burina shi ne na samar da rubutun da zai amfanar da al’umma.

Mun gode da lokacin ki.

Ni ma na gode ƙwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *