Runduna ta ƙaryata labarin kashe sosjoji 20

Daga FATUHU MUSTAPHA

Rundunar Sojojin Nijeriya ta ƙaryata labarin da wata jaridar intanet ta buga mai nuni da ‘yan Boko Haram da mayaƙan ISWAP sun kashe sojoji 20 a yankin Arewa maso-gabas.

A sanarwar da rundunar ta fitar a Alhamis, Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a na rundunar, Brig.-Gen Mohammad Yerima, ya ce wannan labari ba shi da tushe balle makama.

Ya ce an yaɗa labarin ne da manufar sanyaya wa al’umma guiwa game da sha’anin yaƙi da matsalolin tsaro da sojojin ke yi da ma su kansu sojojin da ke yaƙin.

A cewarsa harin baya-bayan nan da aka kai wa sojojin da ke aikin bada tsaro ga ma’aikatan da ke aikin hanyar Goniri-Kafa a ranar 5 ga Fabrairu, da kuma Geidam a ranar 9 ga Fabrairu, jami’ansu sun maida martanin kariya yadda ya kamata.

Ya ci gaba da cewa an samu jami’an da suka rasu sakamakon hare-haren sannan waɗanda suka ji raunuka daga ciki na ci gaba da samun kulawa a asibitin sojoji.

Yerima ya ce Boko Haram da ISWAP na neman mafaka haka ma suna matuƙar buƙatar abinci da magunguna da sauran kayayyakin aiki sakamakon tarwatsa sansanoninsu da sojoji suka yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *