Sarkin waƙa Naziru ya bai wa Ladin Cima kyautar Miliyan biyu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Naziru Ahmed Sarkin Waƙa ya gwangwaje Ladin Cima, wacce aka fi sani da Tambaya, da kyautar Naira miliyan 2 domin ta fara kasuwanci da magance wasu matsalolinta.

Naziru Sarkin Waƙa ya bayyana hakan ne a sahihin shafinsa na Facebook.

A makon da ya gabata ne dai Tambaya, wacce ta daɗe tana harkar fim a masana’antar Kannywood, ta tada ƙura, bayan da ta yi wata hira da BBC Hausa, inda ta ce ba a taɓa ba ta sama da Naira dubu 2 ko 3 idan ta yi fim ba,

Wanda hirar ta haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ‘yan Kannywood ɗin, inda Sarkin Waƙa ya fito ya goyi bayanta.

To, sai kuma ga shi a ranar Lahadi ya wallafa cewa ya ba ta kyautar Naira miliyan biyu domin ta samu ta yi wata sana’ar da za ta riƙe kanta.