Sauya sheƙa: Ƙofarmu a buɗe take ga masu son dawowa APC – Buhari

Daga AISHA ASAS

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ƙofar jam’iyyarsu ta APC a buɗe take ga duk ɗan siyasar da ke sha’awar sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.

Buhari ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook ran Laraba a matsayin tsokaci dangane da sauya sheƙa da Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya yi kwanan nan daga PDP zuwa APC.

Buhari ya ce dawowar Matawalle APC ya nuna cewa ƙudurin shugabanci nagari da suke da shi shi ne dalilin da ya sa ‘yan Nijeriya ke ta rungumar APC.

Don haka ne shugaban ya ce, “Bari in faɗa ƙarara cewa ƙofofinmu a buɗe suke ga sauran ‘yan siyasar da suka yi amanna da ajandarmu ta sake gina Nijeriya.”

Daga nan Buhari ya yi kira ga ɗaukacin gwamnonin APC da ma zaɓaɓɓun ‘yan majalisu a faɗin ƙasa, da su ci gaba da aiki tuƙuru don tabbatar da jam’iyyarsu ba ta rasa tagomashinta ba kana ta ci gaba da riƙe mulki har gaba da 2023.

“Kada mu manta cewa a matsayinmu na zaɓaɓɓu a APC, ayyukanmu a dukkanin matakai za su yi matuƙar tasiri game da makomar jam’iyyar. ‘Yan Nijeriya na sa ran ganin ayyuka da dama daga gare mu kuma ba za mu ba su kunya ba,” in ji Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *