Shan fetur ya ragu zuwa lita miliyan  44.3 kowacce rana a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Amfani da man fetur na cikin gida na ƙasar Nijeriya ya ragu sosai daga litoci miliyan 66.7 da ake sha a kullum a faɗin ƙasar zuwa litoci miliyan 44.3 a kowacce rana. 

Shugaban zartarwa na hukumar kula da man fetur ta NMDPRA, Farouk Ahmed Ahmed shi ya bayyana haka a jawabinsa na buxe taro a taron ‘Oil Trading and Logistics’ (OTL) na makon Afirka na bana, shekarar 2023, da aka gudanar ranar Litinin a jihar Legas.

A cewarsa, an samu raguwar kaso 33.58 a kan yawan man da ake sha a kullum. 

A jawabin nasa, shugaban hukumar ta NMDPRA ya bayyana cewa, takwas daga cikin masu sarin man fetur masu lasisi guda 94, ne kaɗai ne suke samun  damar shigo da mai cikin ƙasar nan.  

Kuma a cewarsa, waɗannan dillalan guda 8 masu lasisi, sun shigo da jirage 8 ɗauke da fetur a wanda ya kama jimillar 251,000 MT wato (litoci 291,238,670.69) a tsakanin watan Yuni da Satumban wannan shekarar. 

Ahmed ya ƙara da cewa, raguwar masu sarin man yana da alaƙa da qalubalen da ake fuskanta a wajen canjin kuɗi wanda ya kawo cikas ga kamfanonin wajen shigo da man. 

Amma a cewarsa, ana sa ran cewa, ƙwararan matakan da gwamnatim take ɗauka zai bunƙasa shigo da man. Yadda wasu ƙarin kamfanonin su ma za su dinga shigo da shi tare da Kamfanin raba man fetur NNPC. 

Ahmed ya ƙara da cewa, samun man fetur zai ƙara bunƙasa ne idan matatar man Ɗangote ta fara aiki sosai, sannan kuma aka gyara matatun man fetur na NNPCL a matsakaicin zango.  

Ahmed ya kuma bayyana cewa, babban ginshiƙin samun mafita game da harkar makamashi a Nijeriya shi ne samar da gas a matsayin madadin makamashi ta hanyar shirin ‘Decade of Gas Program’ (DOGP).

Shirin DOGP shiri ne da zai tabbatar da bunƙasar gas ta hanyar sarrafa shi, adana shi sufurinsa sarar da shi da kuma amfani da shi a Nijeriya,  nan da shekaru 10. Kuma a cewarsa, lamarin yana tafiya yadda ya kamata. 

Ahmed, ya ƙara da cewa, a yanzu haka ma shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da shirin samar da gas ɗin na CNG (PiCNG), da nufin samar da wata hanya ta zamani ta sauƙaƙa samar da makamashi mai ɗorewa.  Kuma abin ya fara garawa ma yanzu.