Shugabannin Sin da Madagascar sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar dake tsakanin ƙasashen su

Daga CMG HAUSA

A yau Lahadi ne shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Madagascar Andry Rajoelina, suka taya juna murnar cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen su.

Cikin sakon sa, shugaba Xi ya ce tun kafuwar wannan dangantaka shekaru 50 da suka gabata, alaƙar sassan biyu ta ci gaba da kyautatuwa bisa daidaito, duk da sauye sauyen da ake samu a harkokin ƙasa da ƙasa.

Ya ce yana dora muhimmancin gaske ga alaƙar dake tsakanin ta da Madagascar, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Rajoelina, wajen amfani da wannan biki, a matsayin wata dama ga ƙasashen, ta ci gaba da daga matsayin haɗin gwiwar kawancen su, da baiwa ƙasashen da al’ummun su damar cin gajiya.

A nasa ɓangare kuwa, shugaba Rajoelina cewa ya yi, tun kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasar sa da Sin shekaru 50 da suka gabata, sassan biyu sun faɗaɗa haɗin gwiwar su a sassa daban daban, an kuma cimma manyan nasarori masu yawa.

Ya ce Madagascar a shirye take, ta yi aiki da Sin wajen ƙarfafa manufar samar da al’umma mai makomar bai daya ta Madagascar da Sin.

Mai fassara: Saminu Alhassan