Sudan: Maƙalallun ‘yan Nijeriya sun isa Abuja

Jirgin saman Air Peace ya yi nasarar kwaso ɗaliban Nijeriya sama 270 daga Filin Jirgin Saman Aswan da ke Masar zuwa Abuja, inda ya sauka Babban Filin Jirgin Saman Nnamdi Azikiwe da misalin ƙarfe 11:38 na dare a ranar Laraba

Haka shi ma jirgin sojojin saman Nijeriya, NAF C-130, ya biyo baya jim kaɗan ɗauke da mutum 80.

An cimma wannan nasarar ce bayan mako guda da bai wa ‘yan ƙasa tabbacin kwaso waɗanda lamarin ya shafa da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Bayanai sun ce, sakamakon rufe sararin samaniyar ƙasar Sudan mai fama da rikici, ya sa aka yi jigilar ɗaliban a motoci zuwa Masar kana daga nan aka kwaso su.