Tambuwal ya ƙaurace wa gangamin Atiku na Bauchi, ya ziyarci Buhari da Bagudu a Abuja

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ƙi halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugabancin ƙasa na jam’iyyarsu ta PDP a Bauchi domin halartar ganawar sirri da wasu gwamnonin APC, sannan daga bisani ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari.

Jaridar News Point Nigeria ta kalato cewa, Tambuwal wanda shi ne Darakta-Janar na kwamitin neman yaƙin zaɓen Shugaban Ƙasa na PDP, ya yi ganawar sirri da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC kuma Gwamnan Jhar Kebbi, Atiku Bagudu tare da tsohon Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi a gidansa da ke Maitama, Abuja.

Majiyarmu ta ce Shugaba Buhari ne ya buƙaci ganawar bayan samun rahoton ƙarar da wasu gwamnonin APC suka shigar kotu kan Gwamnatin Tarayya.
Gwamnonin da lamarin ya shafa su ne; gwamnonin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara.

A cewar majiyar, bayan gwamnonin sun kammala ganawarsu, an ga Tambuwal da Bagudu sun shiga mota guda zuwa Fadar Shugaban Ƙasa.

Ta ci gaba da cewa da fari gwamnonin sun yi ƙudirin zuwa kotu kan batun sabbin kuɗi a farkon wannan mako, amma da damansu sun canza ra’ayi bayan tattaunawar tasu in ban da Gwamna El-Rufai da Gwamna Matawalle da kuma Gwamna Bello na Kogi.

“Buhari ya nuna ɓacin ransa yayin taron, kuma ran nasa ma ya fi ɓacewa a yanzu, saboda duk da kwana bakwai da ya nema don ɗaukar mataki uku daga gwamnonin APC sun yi gaban kansu sun maka Gwamnati a kotu kan batun,” in ji majiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *