Tinubu, Shugaban APC na Ƙasa, Adamu da wasu sun yi ganawar sirri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Sanata Bola Tinubu ya gana da Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu a gidan tsaro da ke Abuja.

A wajen taron da aka gudanar a sirrance akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege; Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Iyiola Omisore da tsohon Sakataren Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugabancin Jam’iyyar APC, Hon James Faleke.

A ƙarshen taron, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa ya ce taron wani aiki ne na yau da kullum. Ya ƙi bayyana batutuwan da aka tattauna a taron.

Ganawar na zuwa ne kwanaki biyu da dawowar Tinubu ƙasar bayan shafe sama da wata guda a Turai.

Za a rantsar da Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa a matsayin wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 29 ga Mayu.

Tinubu ya samu ƙuri’u mafi yawa a zaɓen da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta ayyana shi a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, duk da cewa a halin yanzu manyan ‘yan takara biyu ne ke ƙalubalantar nasararsa a kotun; Jam’iyyar Labour Party (LP) da Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP.