Tinubu ya sha ƙasa a rumfar Tambuwal

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jamiyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya sha ƙasa a rumfar zaɓen Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.

Tinibu ya sha ƙasar ne bayan da abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya doke shi da ƙuri’u 250, yayin da shi kuma ya tsira da ƙuri’u 44.

Tambuwal, Wanda kuma ke takarar kujerar Majalisar Dattawa ya doke Sanata Dan Baba Dambuwa na jamiyyar APC dake kan kujerar da ƙuri’u 252, yayin da Dan Baban ya samu ƙuri’u 44.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *