Tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Mikel Obi ya yi ritaya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon kyaftin ɗin Super Eagles na Nijeriya kuma tsohon ɗan wasan Chelsea, John Mikel Obi, ya sanar da yin murabus daga buga wasan ƙwallon ƙafa.

Obi, wanda ya taka rawar gani a matakin ƙungiya da kuma tawagar ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasarsa, ya yi amfani da shafinsa na Instagram wajen sanar da murabus ɗin nasa a ranar Talatar nan.

Ya ce, a cikin shekaru 20 da ya kwashe yana buga wasan ƙwallon ƙafa, nasarorin da ya samu, ya same su ne tare da goyon bayan iyalansa da manajoji da masu horaswa da abokan wasansa, sannan kuma uwa uba magoya bayansa.

Ɗan wasan na Nijeriya ya samu gagarumar nasara a tsawon shekaru 11 da ya yi a Chelsea, inda ya zura ƙwallaye shida a raga sannan ya taimaka aka zura 13 a wasanni 372 da ya yiwa ƙungiyar.

Ɗan wasan mai shekaru 35 ya lashe kofunan firimiyan Ingila biyu da kofunan FA uku da kofin League a 2007 da kuma gasar Europa ta shekarar 2013.

Ya kuma kasance cikin tawagar Chelsea da ta lashe kofin zakarun Turai a karon farko a shekarar 2012.

A matakin ƙasa kuwa, Obi ya samu nasarar lashewa ƙasarsa Nijeriya gasar kofin nahiyar Afirka a shekarar 2013.