Tun da Hudu ya haɗu da ’yan sanda…

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A ƙarshe dai, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ba da labarin cewa ta kama kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa Barista Hudu Yunusa Ari da tun farko hukumar zaɓen INEC a taƙaice ta dakatar da shi don ayyana sakamakon zaɓe ba tare da hurumin yin hakan ba. Yayin da a ka ɗauka za a ji Ari ya miƙa kansa ga rundunar ko kuma a ce rundunar ta gayyace shi don amsa tambayoyi, sai kwatsam sanarwa daga kakakin rundunar Olumuyiwa Adejobi ta ce ‘yan sanda sun kama Hudu Ari don gudanar da bincike a kan sa da ma wasu da ke da hannu a zargin saɓa dokokin zaɓe a jihar Adamawa.

Sanarwar ba ta bayyana yadda a ka kama Hudu ba amma dai an bayyana cewa zaratan ‘yan sanda masu aikin zaɓe ne su ka kama shi. Gabanin kama shi Hudu ya zanta da wasu manyan kafafen labaru ta hanyar sauti da faifan bidiyo inda ya yi ƙoƙarin wanke kan sa daga zargin da a ke yi ma sa ta hanyar ambata dalilan da su ka saka ya ayyana ’yar takarar APC Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓen gwamnan Adamawa.

Kazalika Hudu ya yi watsi da zargin an ba shi maƙudan kuɗi don murde sakamakon ya na mai cewa sam bai taɓa karɓar ko sisin kobo daga sassan biyu na zaɓen ba.

Kwamishinan bai ja birki a nan ba sai da ya ƙalubalanci duk wanda ya ke ganin ya ba shi toshiyar baki ya kai shi ƙara kotu don shari’a ta yi aikin ta. Wani abu ma da Hudu ya yi shi ne nuna takaicin tava lafiyar wasu daga jami’an zaɓen irin babban kwamishina daga Abuja Farfesa A.A Zuru. Bai kuma nuna wata nadamar matakin na sa ba don ya gwada tamkar ya na da yaƙinin shi ne mai gaskiya.

Baya ga zantawar, Hudu ya rubuta wasiƙa ta musamman ya iakawa babban sufeton ‘yan sanda Usman Baba Alƙali da kuma hukumar zave don su duba kuma wasiƙar ta zama bayanin da zai sauƙaƙa bincike ko ma ya wanke shi.

Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta ce ba ruwan ta da wasiƙar kare kai da kwamishinan ta na Adamawa Barista Ari Yunusa Hudu don ta umurci shi ne ya miƙa kan sa ga babban sufeton ’yan sanda don gudanar da bincike kan ayyana sakamakon zaɓen Adamawa ba da hurumi ba.

INEC na martani ne kan wasiƙar da Hudun ya rubutawa babban sufeton da tura ma ta kofi kan dalilan sa na ayyana sakamakon zaben. Kuma shi ma Hudun ya ce ya ji labarin INEC ta ce ba ta karɓi wasiƙar ba amma ya san ta karɓa.

A zantawar dai bai bayyana muradin san a aika wasiƙar ba maimakon miƙa kansa ga ’yan sanda.

Hukumar wacce dama ta dakatar da Hudu bayan ayyana Sanata Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaɓe, ta buƙaci rundunar ’yan sanda ta gudanar da bincike kan aabubuwan da su ka faru don ɗaukar matakan shari’a.

In ba a manta ba daga nan hukumar ta koma Adamawa ta kammala tattara sakamakon zaɓe da aiyana gwamnan da ke gado Umar Fintiri a matsayin wanda ya samu tazarce.

Jami’a a sashen labarun hukumar Zainab Aminu ta ce INEC ba za ta karɓi ko duba wani saqo daga kwamishinan da a ka dakatar ba sai in an samu sakamakon binciken. Ta ce INEC na buƙatar a binciki Hudu don gano ko abubuwan da ya aikata sun saba ƙa’ida da hakan zai kai ga gurfanar da shi gaban kotu.

Hudu Ari dai ya yi zargin babban baturen zaven da dan rakiya ya gana da gwamnan Adamawa Umar Fintiri a gidan gwamnati don haka ya ga ba za a samu adalci ba; wanda ya sa zuciyarsa ta hakkake ya sanar da sakamakon da ya ce ya na da yaƙinin gaskiyar sakamkon zaɓen kenan.

Hudu bai ma nuna akwai wani abu da sauran sakamako da bai iso ba zai iya yi wajen sauya abun da ya ke hannun sa a lokacin.

A wata amsar ma ya nuna wasu bayanan duk a yanar gizo ya gani kuma abun ya ba shi mamaki kenan yadda mutane kan yanke hukunci da nuna ya yi riga malam masallaci ko ya mashi biliyoyin Naira na cin hanci don fifita wani ɓangare.

In za a tuna gwamna Fintiri da ya ke karɓar shaidar lashe zaɓe ya yi alwashin ɗaukar matakin shari’a kan kwamishinan. Fintiri wanda ya ɗauki alhakin cin zarafin da a ka yi wa wasu daga jami’an zaɓen, ya zayyana Hudu da mutum mai munafurci wanda ya kwari al’ummar Adamawa ko neman tada fitina a jihar Adamawa.

A ganin Fintiri laifin Hudu ya kai duk ‘yan Nijeriya su taru su ɗau mataki a kan sa don kare mulkin dimokraɗiyya “ba zan yafe ba sai na hukunta Hudu”.

Kai tsaye gwamnan bai ɗora wani laifi kan ’yar takarar APC Binani ba, sai dai ya zargi wasu a Abuja da yin amfani da damar wajen biyan muradun kan sa.

Gwamnan ya nuna tamkar ya na gwabzawa ne da wasu ƙusoshi a Abuja da ke son amfani da damar nasarar Binani wajen kare kan su daga wasu laifukan da su ka aikata.

A na su ɓangare magoya bayan ’yar takarar APC Aisha Binani da bayanai ke nuna ta shirya garzayawa kotu, sun ce za su qalubalanci gwamna Fintiri kan sakamakon zaɓen.

Umar Garkuwa na kan gaba a masu hamayya da Fintiri ya ce za su bi duk hanyoyin shari’a don neman dawo mu su da nasara “ina tabbatar ma ka tun da lamarin ya na kotu, ka jira ka gani za a rantsar da Binani” Garkuwa wanda tsohon ɗan canjin kuɗi ne a Abuja da Dubai ya caccaki gwamna Fintiri da nuna zuciyar gwamnan na cike da son ramuwar gaiya ne na abun da ya faru shekaru aru-aru.

Baya ga zantawa da wasiƙar da Hudu ya aikawa hukumomi, za a iya cewa ya fake a wani waje ne don nazartar hanyoyin da zai kare kan sa daga yadda sunan sa ke tambari a kafafen labaru; yayin da ita kuma rundunar ’yan sanda ba ta aiyana neman sa ruwa a jallo ba sai kawai labarin da ta fitar cewa ta kama shi.

Yanzu dai ido ya koma kan rundunar ’yan sanda da ke cewa ta na yi wa Hudu binciken kwakwaf duk da ba ta fadi lokacin kammala binciken ba da kuma abun da zai zama mataki na gaba. Shin za a samu Hudu da laifi ko kuwa zai kare kan sa?

Duk abun da ya fito daga ’yan sandan shi ne zai zama haska wanda ƙaddara za ta fada kan sa mai kyau ko akasin hakan.

A ɓangaren hukumar zave an cika ma ta buƙatar ta ta turke kwamishinan don gudanar da bincike a hukumance.

In a na sharhi kana bun da Hudu ya yin a ayyana sakamakon zaɓe gabanin kammala tattara dukkan sakamako ba farau ba ne a hukumar zaɓe.

A zaben shekara ta 2007 zamanin gwamnatin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo an samu irin wannan yanayi ko yanayin da ya fi haka ban mamaki.

Tsohon shugaban hukumar zaɓe Maurice Iwu ya ayyana sakamakon zaven gabanin kammala tattara sakamako inda hakan ya ba wa marigayi tsohon shugaba Umaru ’Yar’adua na PDP nasara.

Bai ma zama abun mamaki ba don a yaƙin zaɓen, Obasanjo wanda bai samu cimma burin san a tazarce karo na uku ba, ya zayyana zaɓen da ko-a-mutu-ko-a yi-rai. Wato ba ma yadda za a yi PDP ta faɗi zaɓen.

Gabanin zaben 2015 da shugaba Buhari ya lashe, duk dan takarar da ya samu tikiti a PDP na ɗaukar kansa tamkar ya na jiran lokacin rantsuwar shiga ofis ne. Ba mamaki abubuwan da a ka gani a zaɓen nan na 2023 na nun aba lalle don ɗan takara na jam’iyyar gwamnati ne zai iya lashe zaɓe ba.

Cikin ikon Allah a 2007 marigayi shugaba Umaru ’Yar’adua ya ayyana zaɓen sa da cewa an samu matsaloli da ke buqatar gyara kenan. Kuma wannan na da nasaba da yadda a ka ayyana sakamako kafin kammala tattara ƙuri’u. Neman yin gyaran ya sanya ’Yar’adua kafa kwamitin gyaran dokokin zaɓe da tsohon babban alkali Jostis Muhammad Lawal Uwais ya jagoranta. Duk gyaran zave da a ke amfani da shi a yanzu ya hau doron aikin wancan kwamitin ne na Uwais.

Kawai ƙalubalen ba za a iya cewa a na bin dokokin sau da kafa ba. Wata dokar ma za ka taras hatta ‘yan majalisa na samun bambancin matsaya a kai.

Kammalawa;

Ko ma me za a ce Nijeriya ta samu dogon zangon dimokraɗiyya da ya fi na kowane lokaci daga samun ‘yanci a 1960. Daga 1999 zuwa 2023 an samu shekaru 24 cif yayin da a jamhuriya ta farko a ka samu shekaru 6 inda jamhuriya ta biyu a ka samu shekaru 4 kacal sojoji su ka kifar da gwamnatin Shagari shugaba Buhari na yanzu a soja ya haye madafun iko.

Wannan dai nasara ce don kusan kowane ɓangare sun yi mulki wa imma a matakin shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, shugaban Majalisar Dattawa ko wakilai.

Kowa mai ƙaunar Nijeriya ya ƙara tsayin daka don sauyin da a ka samu na zaɓe a 2023 ya ƙara inganci a 2027 ta yadda sai wanda mutane su ka zaɓa ne kaɗai zai hau karaga.