Ubangiji Ya riga ya zaɓi wanda zai zama Gwamnan Kano – Gawuna

Daga RABI’U SANUSI a Kano.

Ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya bayyana cewa Allah Ya riga ya zaɓi wanda zai zama gwamna a Jihar Kano tun fil azal.

Gawuna ya bayyana haka ne yayin da yake kaɗa ƙuri’arsa da safiyar Asabar a mazaɓarsa dake Gidan Nasiru Ahli dake Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Jihar Kano.

Ya ce yana da tabbacin samun nasara a wannan zaɓe wanda a cewarsa yana gudana cikin kwanciyar hankali.

“Ba zan yi ƙasa a gwuiwa ba wajen cewa Ubangiji ke ba da mulki, mun kuma yi zaɓe kamar yadda mutane suka fito suka yi nasu, dan haka muna sa ran samun nasara a ƙarshen zaɓe.”

A ƙarshe, ɗan takarar ya kuma yaba da yanayin fitowar jama’a wajen zaɓen wanda zai wakilce su, ya ce ya zuwa yanzu yana jiran a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

Gawuna ya yi fatan Allah Ya sa hukumar zaɓe ta gyara kura-kuren ta da suka faru a zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gabata.