Wani matashi ya kashe kansa saboda rashin ƙarfin mazaƙuta a Kwara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar NSCDC ta bayyana cewa, wani matashi ɗan shekara 22 mai suna Shuaib Idris ya kashe kansa a garin Gwanara da ke ƙaramar hukumar Baruten a Jihar Kwara saboda rashin ƙarfin iya saduwa da mata.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Babawale Afolabi ya sanya wa hannu, kuma aka miƙa wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Ilorin ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce, ɗaukacin al’ummar da ke zaune a ginin Ankara Wooro, da ke Gwanara, sun shiga cikin makoki a ranar 28 ga watan Oktoba, yayin da aka gano gawar Idris, wani ma’aikacin NCE, wanda ya rataye kansa a jikin bishiyar Kashu.

Ya ƙara da cewa, an cire gawar daga jikin bishiyar aka kaita asibiti domin a gudanar da cikakken bincike, yayin da ake ci gaba da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *