Wani mutum ya kashe almajiri, ya cire ƙwaƙwalwarsa a Bauchi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wani mutum ya yi amfani da dutse wurin fashe kan wani almajiri mai shekaru 11 tare da cire ƙwaƙwalwarsa a yankin Ƙofar Wambai da ke cikin birnin Bauchi.

Mazauna yankin sun ce, wani baƙo ne da ba a san ko wanene ba ya kira wasu ɗaliaban almajirai biyu tare da jan su zuwa wani keɓantaccen wuri inda ya aikata aika-aikar.

Ɗaya daga cikin almajiran wanda ya sha da ƙyar, ya sanar da mazauna yankin abinda ya faru kuma sun hanzarta zuwa wurin amma sai suka tarar da gawar almajirin inda daga bisani suka sanar da ‘yan sanda.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Muhammad Ahmad Wakil, ya ce, ’“yan sanda sun samu kirar gaggawa daga wani mutumin kirki cewa wani mutum ya yi amfani da dutse inda ya fashe kan almajiri.

“Mutumin ne ya yaudari almajiran biyu, Muhammad Yunusa mai shekaru 11 da Aminu Yusuf mai shekaru 12 inda ya yi amfani da dutse tare da fasa kan Muhammad dkn cire ƙwaƙwalwarsa,” inji jami’in ’yan sandan.

Ya tabbatar da cewa, ‘yan sanda suna ƙoƙarin ganin sun cafke mutumin tare da bi wa yaron haƙƙinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *