Assalamu alaikum, kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata cewa, za mu cigaba daga inda muka tsaya.
Abu na biyu da zan gaya muku shi ne yana da kyau ku fahimci cewa waɗannan abubuwa ba a samunsu haka kawai, wato ba sa samun mutum haka kawai, dole ne ku yi ƙoƙari wajen samar da su. Hanyar samar da su kuwa ita ce dukkan ma’auratan su so junansu. Wataƙila ku tambaya ta ya ya?
Kamar yadda ake cewa ne, “ba a iya tabbatar da so da ƙauna ta hanyar ƙarfi da tursasawa”, lalle haka ne don kuwa so kamar ƙaramar bishiya ce, dole ne a bata ruwa da kula da ita, don haka duk wani abin da za ku yi wajen kula da girman wannan bishiya dole ne ku yi hakan wa ƙaunarku. Hakan kuwa yana hannayenku ne Ya ku matasa.
Hanyar da za ku bi wajen cimma wannan abu ita ce ta hanyar ƙauna da biyayya ga junanku da kuma nuna wa abokan zamanku haƙiƙanin so da kula. Ku nuna wa juna cewa rayuwarku ta danganta ne ga junanku, dukkan waɗannan abubuwa za su taimaka wajen ƙarfafa shu’urin soyayya da ke zukatanku.
Babu makawa, kusan dukkan kiraye-kiraye da umarnin da Musulunci yake bayarwa dangane da sanya Hijabi yana yinsu ne saboda kare wannan alaƙa ta aure. Don haka idan har, a matsayinku na matasan da za su yi aure, ba ku kula da hakan ba (hijab) a lokacin da kuka fita waje, ko kuma kuka bari idanuwanku suka koma kan wasu matan ko kuma mazan, zukatanku suka koma ga wasu saɓanin abokan zamanku na aure.
Idan kuka bari har kuka ƙulla alaƙa da wasu mata ko mazajen da ba naku ba waɗanda ku ke gamuwa da su a wurare daban-daban, to babu makawa aurenku na iya shiga cikin mawuyacin hali. Da farko dai abokin zaman naku zai/za ta fara rasa irin sha’awar da ke jawo hankalinsa/ta zuwa gare ka/ta da ke haifar da so da tausasawa. Don kuwa koda a ce mutum yana da irin kyaun da Annabi Yusuf (a.s) yake da shi, to babu makawa bayan wani lokaci zai kasance ba wani baƙon abu ba ga ɗaya abokin zaman. Don haka, kamar misalin wannan bishiya, dole ne a ba ta lokaci wajen kula da wannan so da ƙauna.
Kamar yadda na faɗi ne a baya, bai kamata a ɗauka cewa ana iya samun so da ƙauna cikin ruwan sanyi ba ne, a’a dole ne a yi ƙoƙari kafin a same su. Idan kuka duba a ƙasashen yammaci, a wasu al’ummomi, za mu ga cewa matasa sukan tsoma kawukansu cikin harkokin zinace-zinace kafin aure, wannan shi ya kan sa ba sa yin aure da wuri idan aka kwatantasu da sauran al’ummomi.
A irin waɗannan ƙasashe maza da mata, musamman ma maza, sukan yi zinace-zinace kafin su yi aure, haka ne ya kan sanya auren da suka yi daga baya ba ya zama musu wani baƙon abu, kuma ba wani lamari ne mai muhimmanci ba. Don haka ya ya za a iya kwatanta su da wani matashi musulmin da ya nesanci irin waɗannan muggan ɗabi’u, wanda ya rayu rayuwa ta tsarkaka da mutumci? Shin mahangar waɗannan nau’i biyu na mutane kan aure zai iya kasancewa guda? Shin girmamawarsu ga aure zai kasance guda? Koda wasa.
Wani abu kuma da yake da muhimmanci ku fahimta shi ne cewa babu wani mutum, namiji ne ko mace, (in ba Ma’asumi ba), da ba shi da irin waɗannan rauni da kura-kurai, babu wanda yake ya cika komai. Hakan ne ma ya sa za mu ga cewa dokokin Musulunci suna ƙoƙarin kiyaye alaƙa ne ta aure. Hijabi ma don haka aka yi umarni da shi, don kada mace ta buɗe jikinta ga wasu na daban, kada ta shigo cikin mutane ba tare da suturan da ta dace da mutumci da girma ba, don kada ta tada hankulan wasu na daban, dukkan waɗannan abubuwan janyo hankula an kiyaye su ga abokin zamanta (mijinta).
Don haka ya zama dole, tun ranar farko na auren, ma’abutan biyu su yi ƙoƙari wajen kare wannan so da ƙauna da Allah Ya dasa cikin zukatansu. Ya kamata su yi ƙoƙari wajen ƙara wannan ƙauna da soyayya da kuma ƙarfafa su. Hanyar cimma hakan kuwa, kamar yadda na faɗi ne a baya, ita ce ta hanyar taimakon juna da kiyaye mutumci da manufofin juna. A matsayinsu na ma’aurata biyu, dole ne su kiyaye sirrin juna, kada su faɗe su ga wasu ko da kuwa dangi ko na kurkusa da su ne, dole ne ku kiyaye irin shigar da kuke yi. Idan har kuka kiyaye hakan, to babu makawa za ku ji daɗin zaman aurenku.
Mu haɗu a mako na gaba. Wassalam.
Daga Mustapha Musa Muhammad, 09123302968
Magance matsalar tsaro
Mu na ƙara ba gwamnatoci shawara dangane da samun tubka da warwara ta fuskar magance matsalar tsaro.
Tabbas wasu rahotanni da daɗin ji domin ana samun nasarori kamar hallaka jagororin Boko Haram, Abubakar shekau, da miqa wuyan wasu dubban mabiyansa. Haka rahoton hallaka jagoran ISWAP Albarnawi da kuma wanda aka naɗa magajinsa, baya ga hallaka mutane kamar Buharin Daji da Awwalun Daudawa duka nasara ce.
Abun mamaki daban tsoro yadda a makon ƙarshe na wancen wata Oktoba aka samu gano wata maƙera ta bindiga qirar AK-47 a Jos da ke Jihar Plateau, haka a wata arangama jami’an tsaro a Jihar Kaduna sun wargaza wata maboyar ’yan ta’adda tare da kama wani boka da wasu kayan aikinshi da makamai a rahoton BBC Hausa.
Hakan ke fiddo ƙoƙarin gwamnatoci wajen yaƙar ta’addanci amma da sauran aiki. Magance fatara da talauci tare da fallasa ma su ɗaukar nauyin ta’adda ita ce hanya mai kyau. A qara baza koma a ko ina.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa, Katsina, 07066434519, 08080140820.