Yadda ɗan ƙwallo, Achraf ya sha matarsa tauraruwar fim, Hiba da basilla

Daga AISHA ASAS 

A ‘yan kwanakin nan ne dai kafafen sada zumunta suka yi sabon ango, wanda ya kasance abin sha’awar kowacce uwa, mafi wayo a wurin kowanne magidanci, kuma abin haushin mafi yawa daga cikin mata.

Achraf Hakimi, ɗan wasan tamaula da ya kafa tarihin da ba a taɓa samun sa ba a tsakanin mutane masu suna da shuhura.

Kamar yadda yake sananne a tsakanin ƙasashe da dama idan ka cire Nijeriya, saki wani abu ne mai matuƙar wahalar yi, tare da hasara musamman ma ga miji, domin doka ce, mace na da dama kan wani kaso na dukiyar da mijinta yake da ita a lokacin da ya yi yunƙurin sakin ta, ko ta nemi saki bisa ƙwaƙwarar hujja.

Haka kuma, tana da damar faɗar kason da ta ke so daga wurin mijinta na daga ƙadarori da dukiyar da ya mallaka, kuma za ta iya samun yadda ta ke so matuqar tana da ‘mayen’ lauya da kuma maka-makan hujjojin da zata iya ɗaure shi da su, kamar cin amanar ta ta hanyar neman mata, ko cin zarafin ta da sauransu. 

Da wannan ne mata da dama sukan yi amfani da damar wurin yin auren jari, ta hanyar auren mai kuɗi don samun damar zama masu kuɗi a yayin da suka nemi saki. Wataqila wannan zai iya zama dalilin hallasta yarjejeniya kan dukiya kafin aure da dokar ƙasashen suka yadda da ita, wato prenuptial. 

Prenuptial wata dama ce ta ba wa dukiya kariya da ta samu ‘yanci shekaru masu dama da suka wuce. Yarjejeniyar da za a gudanar tsakanin mai aure da wadda zai aura, kan cewa, idan ƙaddarar rabuwa ta ratsa tsakaninsu, ba za ta iya mallakar wani abu daga dukiyar da yake da ita ba, sai abinda ya yi sha’awar ba ta.

Wannan damar tana da matuƙar tasiri ga rayuwar waɗanda suka yi aure a lokacin da suke da shuhura ko kuɗi, domin ta hanyar ce kawai za su iya bada kariya ga abinda suka tara daga matansu idan sun nemi saki a hukumance. Sai dai fa sau da yawa suna kawar da kai ga wannan damar, wataƙila don hayaƙin soyayya da ke saka maye a kwaƙwalwarsu ne, har suke ba wa zuciya tabbacin wadda suke soyayya ba za ta cutar da su ba, ko son da ta ke masu na tsakani da Allah ne, dukiyar su ba ta gabanta.

Da wannan ne mata da yawa suka sha mazajensu basilla, ta hanyar wawashe kaso mai yawa daga dukiyar da suka jima suna tarawa da guminsu. Duk da cewa, wannan doka na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar aure, musamman kasancewar mace ce a ƙasa a zamantakewar aure, kuma ita aka fi cutarwa a lokuta da dama, don haka ga wasu, za mu iya cewa, sun cancanci kason da za a ba su. Idan mun koma a ɓangaren addinin Musulunci, za mu iya cewa, wannan doka wani abu ce da addini ya so a aikata, bambanci kawai shi bai sanya shi wajibi ba.

Malamai da dama sun yi tafsirin ayar da ta ce, “ku sake su (matanku) bisa kyautatawa,” da cewa, idan ka ƙudiri aniyar sakin matarka, Musulunci ya so ka yi mata ‘yar kyauta da za ta ɗan riƙe ta a rayuwar zawarci, sai dai ba a ce dole ba.

A vangaren ɗan ƙwallo Achraf Hakimi wanda ya auri matar shi, Hiba Abouk, jarumar finafinai, a lokacin da yake da shekaru 19, yayin da ta ke da shekaru 31, ma’ana ta girme shi da shekaru 12. 

Hakimi, kamar kowanne namiji da ke cikin shauƙin so, bai yi yunƙurin ba wa dukiyarsa kariya ba a lokacin da ya auri matarshi, sai dai an ruwaito cewa, tuni kallon kitse ake yi wa rogo ta vangaren dukiya da ake tunanin ya tara sakamakon irin kuɗaɗen da yake samu a wasan tamaula da yake bugawa, domin a zahiri talaka ne tilis.

Dalili; duk wani abu da ya mallaka na maifiyarsa ne a hukumance, a wata majiya ma, har zunzurutun kuɗaɗen da ake biyan sa a matsayin albashi yana shiga ne ta asusun ajiyar mahaifiyar. Yayin da ta ke siya masa duk wani abu da ya buƙata na daga ababen more rayuwa.

Wannan lamari dai bai kasance a bayyane ba har sai a lokacin da matar tasa ta yi muradin raba aurenta da shi tare da buƙatar ya mallaka mata rabin duk abinda ya mallaka.

To fa a daidai nan ne ta fahimci cewa, mijinta kuma uban ‘ya’yanta biyu, shahararren ɗan wasan ƙwallo da ya kasance ɗan wasan ƙwallon na shida da suka fi samun kuɗi a yankin Afrika, ba kowa ba ne face talaka da ko mai gadin gidansu ya fi shi arziki, domin shi yana da albashinsa da suke biyan sa duk wata.

Da wannan ne mutane suke ganin wannan hukuncin na Achraf a matsayin guzurin da ya jima yana tanadi, don irin wannan rana, kuma suke ganin kaifin tunanin nasa ya yi masa amfani, tunda dai kwalliya ta biya kuɗin sabulunta. Ya rufe lalitarsa gam ta hanyar amfani da mahaifiyarsa a matsayin mukullin ƙarfe.

Sai dai a wani ɓangare na masu iya zurfafa tunani za mu ce, akwai yiwuwar dalilin ɗan wasa Achraf ya sava wa tunanin mutane, idan mun yi waiwaye da yadda yake amayar da soyayyar mahaifiyarsa a duk wata dama da ya samu.

Na san mai karatu zai iya amincewa da zance na idan ya yi duba da irin faya-fayen bidiyon da ke rausaya a kafafen sadarwa da dama da ke haska ɗan wasan da mahaifiyarsa a mabambantan wurare da ke nuni da tsananin soyayyar da yake mata, kamar wuraren bikin murnar nasarar cin ƙwallo da za ka tarar da yawa suna zuwa ne da matansu ko budurwarsu, ko kuma su kula matan da aka kawo musamman don su. An haska Hakimi wurare da dama tare da mahaifiyarshi suna rawa ko murnar a tare.

Haka ma a wasu bidiyon, an nuna Achraf na isa ga mahaifiyarshi a lokacin da ya sa ƙwallo a raga don yin murnar tare da ita, ko dai ya sumbace ta, ko ta sumbace shi, tare da rumgume shi, kuma sanin kowa ne an fi samun haka ga matan masu nasarar ko a tsakanin abokan buga wasan nasu. 

Ɗan wasan ya sha bayyana irin sadaukarwar da mahaifiyar tasa ta yi masa, wanda ko da ɗan waɗannan misalai kawai za mu iya kafa hujja wurin dasa yarda da cewa, takan yiwu, ɗan wasa Achraf ya yi wannan hukunci ne don saka alkhairi da alkhairi. Don nuna ɗan halak ne, da ba ya manta alkhairi, don tabbatar wa duniya cewa, babu kamar uwa a duk rayuwar kowanne ɗa ko ‘ya.

Ko ma dai meye dalilin nasa, magidanta sun jinjina masa, tare da kiran sa gwarzon maza da kuma kambun girmamawa, domin ya kawo masu mafita ta wannan ɓangare da ke sa su haƙuri da matansu, don gudun saki da zai yi sanadiyyar girgiza aljihunsu. Don haka suka fara hanzari don ganin sun daki ƙarfe da zafinsa, tun kan ya huce.

Idan mu ka yi duba da waɗannan dalilai, za mu iya mamaki a lokacin da muka ci karo da magidanci, kuma mai shahara da ya ga abinda Achraf ya yi a matsayin laifi.

Shahararren mawaqi Peter Okoye, wanda aka fi sani da Mista P, taura ɗaya cikin biyu da suka haifar da Psquare ya yi zazzafan furuci kan wannan lamari da ya zama darasin tattaunawa a ko’ina ka leƙa a kafafen sada zumunta, sai dai kuwa, da yawa sun yi mamakin irin kalaman mawaƙin, duk da cewa, yana ƙoƙarin bayyana abin da Hakimi ya yi a matsayin kuskure. 

Psquare ya yi Allah wadai da mazan da suka ji daɗin abinda ɗan wasan ya aikata, abinda ya kira da cin amana. Ya kuma ja hankalin mutane kan muhimmancin yarda da abokan zama, inda ya bayyana cewa, “kada ka auri matar da ba ka yarda da ita ba.”

Peter ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda yake cewa, “na yi mamakin yadda maza ke tsalle kan yadda lamarin auren Hakimi da matarsa ya kasance. Duk da cewa, gaskiya na da ɗaci, hakan ba zai hana ni faɗar ta ba, idan ba ka yarda da mace ba, kada ka yi auren zai fi. Ya ka ke tunanin rayuwar mace za ta kasance bayan rabuwa, ko kun fi so ku ga matan a mawuyacin hali bayan rabuwar ku.

Ka tuna matar da ka aminta da ita mai amsa sunan mahaifiya gare ka, ita ma ta taɓa zama matar wani. Ya za ka ji, idan aka yi mata abinda ka yi wa matarka? Kawai zai fi ka auri mahaifiyarka tunda dai ba ka yarda da matarka ba.

Ku kuwa dakarun Hakimi na shafin twitter da ke ƙarfafa masa gwiwa tare da ba shi kariya, Ina muku fatan samun irinsa a matsayin suruki. Kuma sai ku tattara ku auri iyayen baku mata, tunda dai abinda ya aikata ya yi tasiri a wurinku.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *