Yadda sabon Daraktan Hukumar Kula da Hanyoyi na Ƙasa ke canja fasalin hukumar – Mista Kalu Emetu

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

An bayyana sabon Daraktan Hukumar Kula da Hanyoyi na Ƙasa wato Road Traffic Services (DRTS) a turance wato Dokta Abdul-lateef Bello a matsayin ƙwararren shugaba da a cikin watanni ƙalilan da ya yi a matsayin daraktan hukumar ya cimma nasarori da dama dake cigaba da kawo sauyi mai ma’ana da kuma canja fasalin hukumar a yanzu.

Shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar, Kulu Emetu ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da wakilin mu a ofishinsa dake babbar sakatariyar hukumar a Abuja ranar Laraba 24 ga watan Agustan shekarar 2022 da ake ciki.

Ya ce ba shakka duk da an naɗa daraktan a ‘yan kwanakin baya ne wato a watan Maris na shekarar 2022 da ake ciki. Amma kawo yanzu ya cimma ɗimbin nasarori a hukumar waɗanda suka haɗa da tabbatar da adalci da aiki tuƙuru tsakanin ma’aikatan hukumar baki ɗaya da samar da wadatattun ababen hawa dake inganta harkokin hukumar da kyakkyawar dangantaka tsakanin hukumar da sauran masu ruwa da tsaki, inda duk suke cigaba da yaba masa a kullum da sauransu.

Acewarsa bayan hakan daraktan hukumar dokta Abdul-lateef Bello yakan kira tarurrukan masu ruwa da tsaki da sauran al’umma baki ɗaya musamman masu ababen hawa akai-akai inda yake bayyana musu manufofi da tsare-tsaren hukumar don cigaban ƙasa baki ɗaya.

Dangane da matsaloli da hukumar ke fuskanta a yanzu kuwa sai mai magana da yawun hukumar, Kalu Emetu ya bayyana cewa daga cikin su akwai matsalar rashin isassun ma’aikata kasancewa a cewarsa babban birnin tarayya Abuja na cigaba da bunƙasa a kullu-yaimin da hakan ke buƙatar ƙarin ma’aikatansu don gudanar da muhimman ayyukan su na wayar da kawunan al’umma da kuma kiyaye haɗurra da rajistar ababen hawa da sauransu yadda ya dace.

Ya kuma yi amfani da damar inda ya sanar cewa daraktan yana kuma tabbatar da kyakkyawar dangantaka tsakanin hukumar da sauran takwarorin su a fannin inda sau da yawa ma sukan yi aiki tare musamman don tabbatar masu ababen hawa suna bin ƙa’idojin kare haɗurra da suka haɗa da hana gudun fitar hankali da yin biyayya ga dokokin hanyoyin da dai sauransu, inda a ƙarshe ya yi kira na musamman ga al’umma ƙasar nan baki ɗaya musamman masu ababen hawa su cigaba da bai wa hukumar cikakken goyon baya don basu damar cigaba da kare rayuka da dukiyoyin su baki ɗaya kamar yadda suke yi a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *