‘Yan fashi sun cika wa ‘yan ƙungiyar Adamawa United aiki

Daga FATUHU MUSTAPHA

‘Yan ƙungiyar ƙwallon ƙafa na jihar Adamawa, wato Adama United, sun gamu da wasu ‘yan fashi a hanyar Benin zuwa Ore a Juma’ar da ta gabata.

Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna ‘yan fashin sun ƙwace wa ‘yan wasan da jami’an ƙungiyar wasu kayayyakinsu haɗa da kuɗaɗe.

‘Yan wasan suna kan hanyarsu ta zuwa Legas ne domin buga wasan da aka tsara za su buga tare da ƙungiyar MFM a nan Legas inda suka gamu da ‘yan fashin da misalin ƙarfe 11:45pm.

Wannan dai shi ne karo na uku da ake samu wata babbar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Nijeriya ke samun akasi a hanyarsu ta tafiya zuwa wajen buga wasa.

Da farko ya faru ne da Wikki Tourist na jihar Bauchi inda suka tsallake rijiya da baya bayan da motarsu ta kama da wuta. Haka ma abin yake ga ‘yan ƙungiyar Kano Pillars.