Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ribas, sun kama mutanen da ake zargin ‘yan ƙungiyar asiri ne 55 da ke aikata ta’asa a yankin Diobu da ke a garin Fatakwal babban birnin jihar.
An cafke su ne a wata mavoyarsu da ke yankin Diobu a ranar Talata.
Wata majiya da ta buƙaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa, tawagar ‘yan sanda da ke yaƙi da ‘yan ƙungiyar asiri da ke caji ofis ɗin ‘yan sanda na Mile 1 ne suka kama su.
Manhaja ta lura da cewa, kai samamen da kuma kamun an yi ne bayan kwanaki biyar da yin gargadin da rundunar ta yi wa ‘yan ƙungiyar asirin da ke aikata ta’asarsu a yankin na Diobu na buƙatar da su amince da zaman lafiya su kuma tsagaita wuta kan faɗan da suke yi.
Idan ba a manta ba, kimanin mutene 15 ne ‘yan ƙungiyar suka halaka biyo bayan wani rikici da suka yi da wata ƙungiyar asiri a tsakaninsu a yankin na Diobu da ke a garin na Fatakwal.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko ce, ta tabbatar wa da manema labarai kamun a garin Fatakwal.
Ko da ya ke, Grace ba ta faɗi adadin ‘yan ƙungiyar asirin da aka cafke ba a lokacin samamen ba, amma ta bayyana cewa, ‘yansandan sun kai samamen ne, biyo bayan wata hatsaniya da ‘yan ƙungiyar asirin suka yi a yankin.