Yayin da Shugaba Buhari ke cika shekarar ƙarshe na wa’adin mulkinsa…

A ranar 29 ga Mayu, 2022, Shugaba Muhammadu Buhari ya cika shekaru bakwai daga cikin shekaru takwas da aka zaɓe shi a karo na biyu. A daidai wannan lokacin ne a shekara mai zuwa zai kammala wa’adin mulkin da kundin tsarin mulkin ƙasar ya amince da shi na tsawon wa’adi biyu ga duk wanda zai yi aiki a wannan matsayi na siyasa a Nijeriya.

Bisa la’akari da wannan muhimmin cigaba, fadar shugaban ƙasa, a ranar 28 ga Mayu, 2022, ta fitar da takardar da ta kira ‘Takardar Gaskiya: Manyan Nasarorin da aka cimmawa kan Cika Shekaru Bakwai na Gwamnatin Buhari’. Takardar mai shafi 20 mai kusan kalmomi 5,000 ta ba da jerin tasirin Buhari ga Nijeriya, daga sake fasalin majalisa, Dokokin zartarwa, da kuma ayyukan samar da ababen more rayuwa da dama.

Daga cikin nasarorin da gwamnatin ta zayyana akwai na ɓangaren sufuri: layin dogo, tituna, filayen tashi da saukar jiragen sama da tashoshin jiragen ruwa. Sauran sun haɗa da fannin wutar lantarki, gidaje, tattalin arziki na dijital, gyara man fetur da iskar gas, da saka hannun jari a cikin ma’adanai masu ƙarfi da noma. Tabbas, akwai alamun gwamnatin Buhari ta huvvasa a cikin abubuwan da aka bayyana a cikin takardar gaskiya, kuma ko shakka babu shugaban zai bar kyawawan baya a waɗannan wuraren.

To sai dai kuma ga ’yan Nijeriya da dama, abubuwan da ke cikin takardar bayanan sun sha bam-bam da abin da gwamnatin Buhari ta faɗa za ta yi kafin yawanta mulki, duba da alƙawuran ‘canji’ da shugaban ƙasar ya yi a shekarar 2015. Misali a ranar 1 ga Janairu, 2015, a makonni biyu gabanin zaɓen, shugaban ya bayyana abubuwa na musamman da dama waɗanda ya kira ‘canji’ da zai kawo wa ’yan Nijeriya.

Ya ce, “na ɗauki lokaci mai tsawo don yin bayanai yadda za a gane, amma a wannan rana ta musamman, bari in tunatar da ku a cikin gajerun bayanai guda biyar. Canji yana nufin: Ƙasa da za ku yi alfahari da ita a kowane lokaci da kuma ko’ina: inda ake yaqi da cin hanci da rashawa, inda shugabanninku su ke da ladabi da jagoranci tare da hangen nesa a mulki, inda labaranmu za su riƙa yawa a duniya suna bayyana irin cigaban da muka samu a matsayin ƙasa; Nijeriya ta zama ƙasar da iyayenku, iyalai ko abokan arzikinku ba za su riƙa jin tsoron wani abu zai same ku ba, ko kuma ku kuna tsoron wani abu zai iya saminsu; Nijeriya inda ’yan ƙasa ke samun abubuwan da ya kamata kowace ƙasa ta samar:

Ababen more rayuwa masu aiki, kiwon lafiya mai araha ko ma kyauta; mutunta yanayi da cigaba mai ɗorewa, ingantaccen ilimi da za a iya gasa da sauran ƙasashe da tattalin arziki; ƙasar da ke samar da ayyukan yi ga matasanta, tare da rage rashin aikin yi zuwa mafi ƙanƙanta da kuma samar da hanyoyin tsaro ta yadda ba za a bar kowa a baya ba; Nijeriya inda harkar kasuwanci zai bunƙasa, gina tattalin arziki da havaka arzikin kowa.”

To sai dai kuma a lokacin da gwamnati ta fitar da nasarorin da ta samu a makon da ya gabata, takardar bayanan ba ta bayyana nasarorin da ta samu ba a fannonin yaƙi da ta’addanci, cin hanci da rashawa, ilimi, rashin aikin yi, da kuma halin da ake ciki na talauci a Nijeriya, waɗanda su ne abubuwan da ke ci wa ’yan Nijeriya tuwo a ƙwarya. Kuma ga waɗannan fagage musamman a maimakon tafi da su, Buhari ke shan suka sosai kan koma bayan tattalin arziki da zamantakewar Nijeriya a wajen al’umma.

Gaskiya ne a cikin shekara ta farko gwamnatin ta kai farmaki ga mayaƙan Boko Haram a Arewa maso Gabas, inda ta kwato mafi yawan yankunan da ke ƙarƙashin ikon mayaƙan. An kashe ko aka kama da yawa daga cikin shugabannin Boko Haram. Duk waɗannan sun ceci ’yan Nijeriya, musamman mazauna yankin Arewa, da raɗaɗin tashin bama-bamai da tashe-tashen hankula da aka fuskanta a shingayen binciken ababen hawa da gwamnatin da ta shuɗe ta yi.

Har yanzu rikicin Boko Haram bai kai ga kawo ƙarshe ba, kuma a ’yan watannin nan da alama ya sake samun galaba a kansa. Ko mafi muni, ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ’yan fashi da sace-sacen jama’a, waɗanda suka yi wa ƙasar muguwar sarƙa, ya gagara kawo ƙarshe.

Haka kuma, duk da yadda tattalin arzikin ya faɗi ƙasa warwas; basusukan da ake bin Nijeriya ya ƙaru sosai ta yadda sama da kashi 80 na kuɗaɗen shiga ke shiga cikin biyan basussuka. Haɓakar farashin abinci bai tava yin girma ba ko kuma ya daɗe irin na wannnan lokaci.

Rashin aikin yi na matasa yana da ban tsoro sosai don haka ƙididdigansa na da girma; da ƙyar jami’o’i suke buɗe qofa ga ɗalibai a cikin shekaru biyu da suka gabata, a gefe guda; kuma idan aka yi la’akari da bayanan baya-bayan nan, nasarorin da aka fara samu a fannin yaƙi da cin hanci da rashawa mai yiwuwa sun lalace. Babu shakka cutar Korona ta yi tasiri akan tattalin arzikin da kuma rugujewar farashin mai a lokacin 2014-2017, inda suma sun ba da gudunmawa ga waɗannan abubuwan.

Abin farin ciki, har yanzu wannan gwamnatin tana da sauran shekara guda; inda ta ke da damar fara ɗaukar matakan gyara a wani yanki mai muhimmanci kamar tsaro. ’Yan Nijeriya sun cancanci ’yancin rayuwa da tsarin mulki ya ba su, amma tashe-tashen hankula daga arewa zuwa kudu, ya kawo cikas ga wannan ’yancin, ta yadda jama’a ke rayuwa da tafiye-tafiye cikin firgici da tsoron kada a yi garkuwa da su, ko a raunata su, ko a kashe su ko a kwace musu dukiyarsu ta tafiyar da rayuwarsu.

Dole ne gwamnati ta juya duk waɗannan a lokacin da ta rage. Dole ne Shugaba Buhari ya yi amfani da duk wata hanya da ofishinsa ke bi wajen magance matsalar rashin tsaro da kashe-kashen rayuka da kare ƙasar da al’ummarta gari. Wannan ajanda mai ma’ana guda yana iya kasancewa kuma dole ne a yi shi.