Zaɓen 2023: Buhari ya cika alƙawarin da ya ɗauka – Gwamnatin Tarayya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamnatin Tarayya ta ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya cika alƙawarin da ya ɗauka na gudanar da sahihin zaɓen 2023.

Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a birnin Washington DC a lokacin da yake ganawa da wasu ƙungiyoyin yaɗa labarai na duniya.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa ministan ya je Washington ne domin tattaunawa da ƙungiyoyin yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa da masu tunani kan zaɓen 2023 da aka kammala.

NAN ta kuma ruwaito cewa kawo yanzu ministan ya yi gana da “Washington Post”, Muryar Amurka, Associated Press da Mujallar manufofin ƙasashen waje.

Ministan ya ce Buhari ya cika alƙawarin da ya yi na dawo da sahihin zaɓe, ya yanke shawarar cewa ba zai bai wa wata jam’iyyar siyasa dama ta musamman ba, ciki har da Jam’iyyar APC mai mulki a lokacin zaɓen.

Ya ce a lokacin zaɓukan da suka gabata, shugaban ƙasar ya tabbatar da cewa babu wanda ya yi amfani da jami’an tsaro wajen maguɗin zaɓe amma ya samar da daidaito wajen gudanar da zaɓen.

“Misalin wannan alƙawari, shi ne jam’iyyar shugaban ƙasa ta daɗi zaɓen shugaban ƙasa a Katsina, jiharsa ta haihuwa.

“Haka zalika, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya sha kaye a jiharsa ta Legas, yayin da shugaban jam’iyyar, Abdulahi Adamu, ya sha kaye a jihar Nasarawa a hannun Jam’iyyar LP.

“Shugaban ƙungiyar yaƙin neman zaɓen jam’iyyarmu ma ya sha kaye a hannun PDP a Jihar Filato.

“Babu wani abu da ya ba wannan zaɓen ya koyar face gaskiya, saboda babu wani maguɗi a jihohinmu,” inji shi.

Ministan ya ƙara da cewa jam’iyyar APC ta sha kaye a jihohi huɗu da suka fi yawan ƙuri’u a zaɓuka; Katsina, Kano, Kaduna da kuma Legas ko a lokacin da jam’iyyar ke riƙe da madafun iko.

Mohammed, ya ce zarge-zargen da ake yi na zamba da ‘yan adawa da masu zanga-zangar suka yi, bai taka kara ya karya ba.

A cewar ministan, rikicin ya samo asali ne saboda gazawar hukumar zaɓe ta INEC wajen ɗora sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na ainihi a kan lokacin.