Zaɓen fidda gwani: Malagi ya taya Bago murna, ya roƙi magoya bayansa su kwantar da hankalinsu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mawallafin jaridun Blueprint da Manhaja, kuma fitaccen ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Neja a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Alhaji Mohammed Idris Malagi (Kaakaki Nupe), ya taya Hon. Mohammed Umar Bago murna yin nasara a zaɓen fidda gwani da ya gudana rana Alhamis ɗin nan.

Yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a Minna, Malagi ya yi kira gare su da su kwantar da hankulansu kuma su cigaba da bai wa Jam’iyyar APC duk wata gudunmuwar da ta dace don ganin an kai ga nasara a babban zaven shekara mai zuwa.

A cewarsa Malagi, “mun amince da zaɓen fidda gwani da aka yi, wanda daliget suka yanke shawarar, wanda kuma dukkansu mambobin jam’iyyarmu ne, mutum ɗaya ya yi nasara, kuma ni tunda na taya wanda ya yi nasara murna; dole ne mu ɗauki ƙaddara mu kwantar da hankalinmu, mu yi aiki tare ga ɓangaren Hon. Umar Bago don ganin ya lashe zaɓen gwamna a jihar a 2023.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *