Zaɓen gwamna a Katsina cike yake da maguɗi – Lado

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar PDP a zaɓen da ya gabata, Sanata Yakubu Lado Ɗan Marke, ya yi watsi da sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta bayyana.

Cikin wata hira da ya yi da BBC, Sanata Lado, ya ce, zaɓe ne mai cike da maguɗi da aringizon ƙuri’u da barazana ga masu zaɓe, da dai duk wani ha’incin da bai taɓa gani a harkar zaɓe ba.

Ya ce, “Ba mu gamsu da wannan sakamakon zaɓen ba tun da mun san ba abin da al’umma suka zaɓa ba ne aka bayyana.”

Ɗan takarar ya ce, ya kamata a daina a koma yin naɗi kawai, saboda a ganinsa hakan ya fi alheri.

“‘Yar manuniya ta nuna ko a lokacin yaƙin neman zaɓe, domin duk inda jam’iyyar APC ta je kamfe ba ta ji da daɗi saboda mutane sun gaji da ita, amma mu duk inda muka je maraba ake da mu,” in ji shi.

Kazalika, ya ce “a zaɓen shugaban ƙasa ai an ga abin da ya faru, suna kan mulki amma sai da muka kada su.

“Idan aka lura ai za a ga cewa mutane a Katsina ba su fito zaɓen gwamna sosai ba, saboda haushin abin da aka yi musu a lokacin zaɓen Shugaban Ƙasa, saboda abin da suka zaɓa ba shi aka ba su ba.

“Babu kunya ba tsaron Allah aka ninka ƙuri’u don kawai su samu nasara, wanda kuma kowa ya san cewa a zaɓen gwamna sam mutane ba su fito sosai ba.”

“Gaskiya za ta bayyana, domin muna wannan gwagwarmayar ne ba don kanmu ba sai don al’ummar jihar Katsina,” in ji Ɗanmarke.

Ya ce, su ba za su yi wani abu da zai saɓa wa doka ba, za su yi abin da doka ta tanada, mutane su kwantar da hankulansu za a yi duka abin da ya dace don ƙwato wa al’ummar jihar Katsina haƙƙinsu.