Zaɓen Peter Obi

Daga MUHAMMAD M. MUSTAPHA

A matakin farko, bayan Hijirarsa zuwa garin Madina Haskakkiya, Annabi Muhammadu SAW ya rubuta yarjejeniyar zamantakewa, don tabbatar da zaman lafiya da lumana. Ya zo a cikin wannan yarjejeniya, kamar yadda Malam Ibnu Hisham ya bayyana a littafinsa Assirah Annabawiyya, cewa: ‘tabbas Yahudawan Banu Auf al’umma ɗaya ne tare da Muminai, Yahudawa su yi addininsu Musulmi ma su yi addininsu. Haka Yahudawan Banun Najar, Banul Haris, Banu Sa’idah…..duk al’umma ɗaya ne tare da Muminai’.

Hakana wannan yarjejeniya ta ci gaba da bayanin haɗaka ta taimakekeniyar rayuwa a tsakanin wannan al’umma ɗaya masu mabanbantan addinai: kowa a cikinsu, matuƙar ya yadda da wannan yarjejeniya, zai nufi ɗan uwansa da alkhairi, abinda takardar ta kira da ‘annus’hu wan nasiha’, kuma wanda za a taimaka kawai shi ne wanda aka zalunta ko a wane addini yake, haka kuma wajibi ne a kan ɗan kowane addini ya taimaki ɗan ɗaya addinin yayin da abokan gaba suka far masa, da ma sauran bayanai na taimakekeniya waɗanda yarjejeniyar ta ƙunsa masu yawa, masu nuna girmamawa ga mutumtaka da ’yancin addini.

Wannan yarjejeniya, wacce Malaman zamani suka fi so su kira da ‘Madina Constitution’, wuƙar gindi ce, kamar yadda fitila ce ga Musulmi ɗan Nijeriya da ma kowane Musulmi a duniya, musamman a wannan zamanin na mu da Turawa ke kira da Postmodern Era; zamanin iya zama da mabanbantan addinai, al’adu da hange-hangen rayuwa daga mabanbantan matsayai a guri guda, zamanin haɗuwar banbanci a cibiya ɗaya. (Na’am, ba tare da ƙaƙaba wa mutum abinda addininsa bai yadda da shi ba!).

Kamar yadda wannan yarjejeniya tana nuni izuwa adalcin Musulunci, rahmarsa, lumanarsa, dacewarsa da yanayin kowane ɗan Adam a kowane zamani da kowace nahiya da kuma manufarsa ta ‘La ikraha fiddin’. Kuma a kan haka, alhamdlillahi, tarbiyyar kusan gaba ɗaya Musulman Nijeriya ta ke.

Sai dai a iya cewa wata tufka da ya kamata a yi wa hanci tun da sanyin safiya, tana ƙoƙarin tasowa ne bayan zaɓen shugancin qasa, wanda jama’ar Nijeriya suka kaɗa a Ranar Asabar 25 ga Febrarun wannan Shekara. A inda nau’in ƙuri’un da aka kaɗa wa ɗan takarar Jam’iyyar Labour Party, Mr Peter Obi, duk da cewa ya sha kayi a bayan Ahmad Bola Tinubu wanda ya lashe zaɓen na jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP, na naiman canja akalar siyasar Nijeriya a matakin tarayya zuwa wata hanya mai haɗari.

Nijeriya ƙasa ce mai mabanbantan addinai da yawa, mafi ƙarfi, rinjaye da yawa a cikinsu Musulunci da Kiristanci. Da yawan mutane, a wannan zaɓe da aka gudanar, suna zargin cewa ƙuri’un da aka kaɗa wa Mista Peter Obi, tare da cewa basu kai shi ga gaci ba, ba wani abu bane face yunƙuri na yawanci na mabiya addinin Kirista daga sassan Nijeriya gaba ɗaya, da haɗe kai waje guda don zaɓo shugaban ƙasa daga ɓangarensu.

Da wannan yunquri ya yi nasara, bisa wannan zato, da jagoranci a Nijeriya kan iya komawa na addini zalla. Wannan yunƙuri, idan wannan zato ya tabbata, kuskure ne babba, da buɗe kafa ga sauran addinai musamman Musulunci wajen kwaikwaya irin wannan yunƙuri, wanda ba zai haifi ɗa mai ido ba. Bugu da ƙari, hakan karan tsaye ne, kuma karya dokokin gyararren kundun tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya ne.

A doka mai lamba 222 (b) akwai nuni izuwa haramcin samar da jam’iyyar siyasa wacce ta talaita kanta da wasu mutane ban da wasu mutanen, da wani yankin ban da wani ko wasu yankunan, da wata ƙabilar banda wata ko wasu ƙabilun, da wani addinin banda wani ko wasu addinan. Wannan doka doka ce ta tabbatar da lumana mai ɗorewa a tarayyar Nijeriya.

Wannan ke nan, a hannu guda kuma a kwai martani da yawa, na jama’a game da wannan lamari, wanɗanda aka yi gaggawar furta wasu cikin kishi da fushi ba tare da an zurfafa tunani ba; na malamai, kasancewarsu fitila a cikin al’umma, shi ya fi haɗari. An ta yaɗa maganganu da dama a kafofin sada zumunta a ciki wasu na cewa: saƙon Kiristoci ya zo musu a fayyace, har ma sun fahimci abinda a da basu fahimta ba, kuma a kaikaice tamkar su ma suna umartar duk Musulman Nijeriya wajibi (na Wasila) da su aikata irin abinda ake zargin mutanen Peter Obi da shi a zaɓe mai zuwa.

Wataƙila da masu irin wannan ra’ayin, afanallahu wa iyyahum, sun lura da haɗarin da ya ke tattare da irin wannan ‘sabon’ tsarin siyasa da ya ke ƙoƙarin kunno kai a Nijeriya da sun kauce wa irin waɗannan maganganun. Domin a zato, wannan tsarin idan ya yi nasara a nan gaba, hakan ka iya samar da Gwamnatin Musulmai ko Gwamnatin Kiristoci: Musulmai su zaɓi Musulmi, Kiristoci su zaɓi Kirista, bisa fatawoyin wajibci daga Masallatai da Majami’o’i.

Kowa kuma a wurinsa addininsa shi ne dai dai. Al-Ƙur’ani Mai Girma yana cewa da mu: ”hakana muka qawata ga kowace al’umma ayyukansu”. A wata Ayar kuma ”kowacce ƙungiya tana alfahari da abinda take da shi”. Ma’ana kowa na ganin kyawu da dai-dai na addininsa. Wannan zai jawo cewa daga wani addinin ya samu nasarar lashe zaɓe, to ɗaya addinin a imaninsa zai ga shi ya fi cancanta ya yi jagoranci ba ɗayan ba. Daga nan sai hassada daga ɓangaren addinin da ya daɗi a zaɓe, sai kuma qiyayya daga ɓangaren addinin da yayi nasara, bisa hujjar mai yasa za a yi masa hassada.

Daga hassada da ƙiyayya sun haɗu ta vangarorin jama’u guda biyu kuwa, to babu abinda zai hana ɓarkewar ƙazamin yaqi a tsakaninsu daga an samu wani ɗan dalili ko mai ƙanƙatarsa, ko da kuwa ɓarar da kaskon ƙosai ne a gefen titi a bisa kuskure. Annabi Muhammadu SAW ya gargaɗi al’ummarsa, kamar yadda Malam Bazzaru ya rawaito, Malam Haisami ya ambata a ‘Mu’ujamuzzawa’id’, da cewa: ‘Cututtukan Mutanen da suka zo kafin ku sun fara dudduqo wa izuwa gare ku: ƙiyayya da hassada’. Da waɗannan munanan ɗabi’u guda biyu ne, hassada da ƙiyayya, ake iya gano dalilai na ɓarkewar yaƙe-yaƙe, tashe-tashen hankula da kuma hanyoyin magance su a Musulunci.

Haka kuma, Mai yiwuwa ne, masu mayar da irin wannan martani na gamo-da-kasawa, basu lura da cewa ta iya yiwuwa da akwai wasu abubuwa da suka shige kuma suka kuɗe can cikin ƙwaƙwalan mutanen Mr Peter Obi da ire-irensu ba, can cikin abinda Malaman Falsafar Psychoanalysis kan iya kira da unconsciousness na su, waɗanda za su iya hana su fahimtar cewa Muslim-Muslim ticket (Tinubu-Shattima), wanda ’yan siyasa suka kawo, ba shi da alaƙa da addinin Musulunci, komar ’yan siyasa ce kawai ta kamun kifi.

Irin waɗannan abubuwa za su iya haɗar da kura-kuren da wasu suka aikata da yawa da sunan addini, wanda hakan zai iya yin tasiri ga abokan zama Kirista. Alal misali, a shekarun baya, wani fefen bidiyo da ya yi ta yawo a kafofin sada zumunta a inda aka ga wani malami na addu’ar Allah ya rusa wata jam’iyyar siyasa wacce ta ke kafira! (Wanda alal haƙiƙa, babu wata jam’iyya kafira, babu wata jam’iyya Musulma, jam’iyya ta haɗakar ƙasa ce) Daga baya kuma sai ga shi a sabuwar jam’iyya mai mulki a matsayin jagora – wannan kan iya aika buɗaɗɗen saao cikin ƙwaƙwalan mabiya sauran addinai har kuma ya zo da irin wannan yunƙuri na mutanen Mista Peter Obi.

Babban aikin Malamai a yanzu amfani da koyarwa da fahimtar addini madaidaiciya (Alkhiɗab Addini Alwasaɗi) tare da yaɗa babbar munufar Addinin Musulunci ta zaman lafiya da lumana haɗi da bayyana wa Musulmai da wanda ba Musulmai ba babban saƙon Annabi Muhammadu SAW na ‘wa ma arsalnaka illa rahmatal lil alamin.

A Suratul Mumtahina, Allah SWT yana horar mu da mu kyautata wa waɗanda ba Musulmai ba, matuƙar ba kashe mu su ke ba, idan mun kyautata musu ma Allah zai so mu. (Kuma da haka ne Musulunci ya yaɗu a mafi rinjaye na sassan duniya a tarihi). A wata Ayar kuma, Allah SWT rantse mana yake cewa mafi kusanci a wajen ƙaunar Muminai su ne Nasara.

Wa haza, Wassalam.