Zan ɗora daga inda Shugaba Buhari ya tsaya – Osinbanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana tsayawa takarar ce a wani jawabi ta bidiyo da aka yaɗa ta talabijin, inda ya yi bayanin irin abubuwan da zai yi idan ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce yana neman tsayawa takarar ce domin inganta rayuwar ‘yan ƙasar, yana mai cewa a matsayinsa na mataimakin shugaban ƙasa yana da ƙwarewar shugabancin Nijeriya.

“A cikin shekara bakwai, na bauta wa gwamnati a matakai daban-daban, kuma bisa umarnin shugaban ƙasa, na wakilci ƙasar nan a muhimman ɓangarori a ƙasashen waje. Na ziyarci kusan kafatanin ƙananan hukumomin Nijeriya. Na je kasuwanni, da masana’antu, da makarantu da gonaki,” inji Osinbajo.

Ya ƙara da cewa ya je gidajen talakawan ƙasar a yankuna daban-daba, sannan “na tattauna da ƙwararru a ɓangaren fasaha a Legas, Edo, da Kaduna; da kuma taurarin Nollywood da Kannywood; da mawaƙa daga Legas, Onitsha, da kuma Kano. Kuma na yi magana da ƙanana da manyan ‘yan kasuwa.”

Osinbanjo ya ce ya samu wannan ƙwarewa ce domin ta zama silar fahimtar matsalolon Nijeriya da kuma yadda zai magance su.

Baya ga kewaya da zai yi jihohi domin neman magoya baya, ‘yan kwamitin yaqin neman zaɓen sa za su shirya ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a domin tattara shawarwari game da matakin da ya ɗauka na tsayawa takarar a zaɓen 2023.

Ana ganin Farfesa Osinbajo zai samu magoya baya, amma yadda zai ɓullo a siyasance ya ƙalubalanci manyan masu sha’awar takarar biyu Bola Tinubu da Mista Rotimi Amaechi, shi ne abin jira a gani.

Rahotanni sun ce kafin sakin bidiyon da za a yi a ranar Litinin, sai da Osinbajo, ya yi buɗa baki tare da gwamnonin jam’iyyar APC a gidansa.

Tuni dai Osinbajo ya buɗe ofishin kamfen ɗinsa a Wuse da ke Abuja.