Ƙarin kuɗin mai: Cikin ’yan Nijeriya ya ɗuri ruwa

*Fetur na iya tashi zuwa Naira 340 lita guda – Shugaban NNPC
*Za mu ba da tallafin sufurin Naira 5,000 duk wata, inji gwamnati
*Babu tanadi a kasafin 2022 – Majalisar Dattawa
*Matakin zai haifar da cin hanci da rashawa – Masu ruwa da tsaki
*Yadda NNPC ke kashe Naira tiriliyan 1.8 akan tallafi duk shekara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Cikin mafi yawan ’yan Nijeriya ya ɗuri ruwa kan makomarsu muddin cire tallafin man fetur bakiɗaya ya kankama nan da watanni.

Tun bayan samun sanarwar daga Gwamnatin Tarayya da ke tabbatar da cewa, a watannin farko na shekarar 2022 za a cire tallafin mai baki ɗaya ake ta guna-guni da cece-kuce.

Ministar Kuɗi, kasafin kuɗi da tsare-tsaren ƙasa, Zainab Ahmed ta bayyana cewa, tallafin ba ya amfanar talakawa, wanda hakan ya sa gwamnati ta cire tallafin man fetur da lantarki cikin tsare-tsaren kuɗinta na 2022.

Ta yi nuni da cewa, farashin man fetur zai yi tashin gwauron zabi kafin watan Yunin 2022, kamar yadda dokar masana’antar man fetur (PIA) ta tanada.

Hukumar Masana’antar Man Fetur da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu a ranar 16 ga watan Agusta, 2021, ta tanadi cire tallafin man fetur a cikin watanni shida da aiwatar da dokar.

Babban Manajan Darakta na Kamfanin NNPC, Malam Mele Kyari, da ya ke magana a wajen taron ya ce, farashin man fetur na iya tashi zuwa Naira 340 a kowane lita idan an cire tallafin.

Domin rage tasirin cire tallafin, Ministar Kuɗi ta ce, Gwamnatin Tarayya za a koma bai wa ’yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi tallafin sufuri na Naira dubu biyar-biyar a kowanne wata.
Ministar ta ƙiyasta cewa, kimanin ’yan Nijeriya miliyan 30 zuwa 40 ne waɗanda suka fi fama da talauci a ƙasar, za su samu tallafin.

Kafafen sadarwa da dama ciki har da Daily Trust sun ruwaito cewa, nazarin shawarwarin ya nuna cewa, Naira dubu biyar-biyar ɗin da za a bayar ga ’yan Nijeriya miliyan 40, gwamnati za ta kashe Naira biliyan 200 duk wata, wanda hakan zai kai Naira tiriliyan 2.4 a cikin watanni 12 na shirin (shekara ɗaya).

Ana shirya wannan tsari ne duk da kura-kuran da aka samu a cikin bayanan ƙasa don tantance mafi talaucin ’yan Nijeriya, inda masana ke nuna shakku kan ikirarin gwamnati na yin rijistar zamantakewar al’umma.

A watan Maris ɗin wannan shekarar, babban sakataren ma’aikatar jin qai, rage raɗaɗin bala’o’i da ci gaban al’umma, Alhaji Bashir Alkali, ya ce, ’yan Nijeriya miliyan 30 ne kawai aka saka a cikin rajistar jin daɗin jama’a na ƙasa daga jihohi 36 da babban birnin tarayya, Abuja, wanda akwai gidaje miliyan bakwai na matalauta da marasa galihu.

Ministan kuɗi a ranar Laraba ta ce, har yanzu gwamnati ba ta tantance hanyoyin gudanar da ayyukan jin ƙai ba.

Da ta ke ƙarin haske kan sanarwar bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a ranar Larabar da ta gabata, ministar kuɗin ta ce, tallafin sufurin Naira 5,000 da aka shirya wa talakawan Nijeriya duk wata zai ɗauki tsawon watanni shida zuwa 12.

A halin da ake ciki kuma, kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin kuɗi ta ce, babu wani tanadin tallafin sufuri na Naira 5,000 ga talakawan Nijeriya miliyan 40 a duk wata a cikin kasafin kuɗin 2022 da majalisar dokokin ƙasar ke tantancewa a halin yanzu.

Shugaban kwamitin, Sanata Adeola Olamilekan Solomon ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ya gabatar da rahoton kwamitinsa kan kasafin kuɗin 2022 ga kwamitin kasafin kuɗi.

Ya ce, kafin hukumar zartarwa ta fara aiwatar da wannan katsalandan, dole ne a aika da shawara kan hakan ga majalisar dokokin ƙasar domin amincewa.

Ya kuma yi tambayoyi game da ƙa’idojin zaɓar waɗanda za su ci gajiyar tallafin sufurin.

Tallafin sufurin wata-wata koto ne ga talakawa, inji ƙungiyar kwadago:
Ƙungiyar Kwadago, a martanin da ta mayar a ranar Laraba, ta bayyana bayyana batun tallafin sufuri na wata-wata a matsayin koto ga talakawa.

Shugaban ƙungiyar kwadagon Nijeriya (NLC), Ayuba Wabba, a wata sanarwa da ya fitar a daren Taraba ya ce, ma’aikatan Nijeriya sun qi amincewa da matsayin Gwamnatin Tarayya na cire tallafin gaba ɗaya.

Ya ce, “martanin ƙungiyar kwadago ta Nijeriya shi ne, abin da muke ji shi ne tattaunawar da Gwamnatin Tarayya ke yi da cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa.

“Tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da al’ummar Nijeriya musamman ma’aikata a ƙarƙashin ƙungiyar ƙwadago a kan batun tallafin man fetur an ɗage zaman ne watanni da dama da suka gabata. Bisa la’akari da firgicin da ake fama da shi a duk faɗin ƙasar da ya biyo bayan bayyana ra’ayin ɗaya daga cikin hanyoyin gwamnati da na ƙasashen waje, ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya na fatan cewa ta ci gaba da yin watsi da matakin da ta ɗauka bisa tsarin shigo da kaya daga waje,” inji shi.

A halin da ake ciki, martani daban-daban sun biyo bayan sanarwar inda wasu masana ke cewa matakin na iya haifar da zamba a tsakanin jami’ai.

Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, shi buqatar talaka ita ce, kar a ƙara kuɗin man fetur ko da kuwa an cire tallafin ko akasin hakan.

Sanata ya ce, cire tallafin na tabbatar da komai zai ƙaru, kama daga kuɗin makaranta da gidajen haya da abinci da kuɗaɗen wuta da makamantansu.

Ya ƙara da cewa, akwai hanyoyin da za a iya bi wajen cire tallafin ba tare da talaka ya shiga tasku ba, musamman idan za a raya matatun man ƙasar da rage kuɗaɗen shigo da mai daga ƙetare.

Sanata Shehu Sani ya kuma nuna rashin gamsuwarsa da tsarin raba wa talaka Naira dubu biyar kowanne wata da sunan rage raɗaɗin cire tallafin mai.

A hirar da wakilin Manhaja ya yi da wata malama a jami’ar Kaduna polytechnic, wacce ta nemi da a sakaya sunanta, ta bayyana cewa, “duk gwamnatin da a ka kafa a Nijeriya sai ta sanar da shirin janye tallafin mai da kuma ƙarin farashin mai a Nijeriya. A duk lokacin da wani shugaba ya ke neman mulki a Nijeriya sai ya lasawa talaka zuma a baki da cewar, zai rage farashin man fetur domin talaka ya sami sauki. Amma da shugaba ya haye karagar mulki sai ya fara maganar janye tallafin mai ko kuma ya ƙara farashin mai, yayin da haka ya ke firgita talakan Nijeriya.”

Ta ci gaba da cewa, “’yan Nijeriya sun fahinci cewar ba wannan ne karo na farko da a ka tava yin ƙarin farashin mai a Nijeriya ba. Domin duk lokacin da wani shugaba ya fito fili ya fara maganar tallafin mai ko ƙarin kuɗin man fetur hankalin ‘yan Nijeriya na tashi.”

Ta ce, batun Naira dubu biyar na tallafin sufuri kuma, mu sani cewa, dubu biyar ba za ta saya wa mutum abin kirki ba ko biyan haya ko sayen abinci.

Ta ƙara da cewa, tsarin gwamnati na kare manufarta da sunan samun kuɗaɗen yi wa talaka aiki, amma a zahiri ƙarshenta kuɗaɗen a karkatar da su maimakon ayyukan cigaban ƙasa.

Sannan sanatan ya tavo batun kuɗaɗen bashi da ake karva a kullum yana mai cewa, har yanzu babu wani sauyi in ban da ƙarin matsalolin kan ’yan ƙaasa.

A halin yanzu dai kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) ne ke biyan wannan tallafin domin ita ce kaɗai mai shigo da mai.

Yayin da ta sanya tallafin man fetur na wata-wata a matsayin hanyar dawo da gazawar man fetur, yana cire jimlar kuɗaɗen da ake fitarwa a duk wata daga kuɗaɗen man fetur da yake yi wa asusun tarayya.

Alqaluman biyan tallafin da kamfanin mai na ƙasa NNPC ya yi, ya yi kaɗan a shekarun baya, amma bisa ga rahoton da aka fitar a watan Oktoban 2021, kamfanin na NNPC ya ce, ya kashe Naira biliyan 864.074 daga watan Fabrairu zuwa Satumba na wannan shekara.

A kan kuɗi na watanni 12, da kamfanin zai kashe Naira tiriliyan 1.8 a shekara guda don tallafa wa man fetur da ajiye shi a kan Naira 162 zuwa 165 a kowane lita a halin yanzu.

Yadda irin wannan shirin cire tallafin ya laƙume sama da Naira biliyan 453:
A shekarar 2012, gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan ta gabatar da wani ɓangare na cire tallafin man fetur.

A madadin tallafin, gwamnati ta ƙaddamar da shirin tallafa wa na ‘Reinvestment and Empowerment Programme’ da aka fi sani da ‘SURE-P’ wanda ta ce, shi ne batun sake saka hannun jarin Gwamnatin Tarayya daga asusun cire tallafin man fetur kan muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa da tsare-tsare na zamantakewar al’umma.

An ce, shirin ya laƙume sama da Naira tiriliyan 453.8 a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013 ƙarƙashin kulawar shugaban majagaba, Dakta Christopher Kolade wanda ya tafi a watan Satumban 2013 ya miqa wa Janar Martin Luther Agwai, daga baya kuma Ishaya Dare Akau ya maye gurbinsa.

Takardu daga ofishin babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin jama’a na lokacin, Doyin Okupe, ya nuna cewa, gwamnati ta kashe sama da Naira biliyan N453.8 tsakanin shekarar 2012 zuwa 2013. Yayin da Gwamnatin Tarayya ta samu kashi 41 cikin 100 na asusun, jihohi da kuma ƙananan hukumomi sun samu kashi 59%.

A shekarar 2012, gwamnati ta yi amfani da Naira biliyan 38.44 da kuma wani Naira biliyan 40.83 a shekarar 2013 akan ‘Social Safety Nets’ kamar lafiyar mata da yara, zirga-zirgar jama’a, ayyukan hidimta wa al’umma da tsarin horon digiri. An kuma yi amfani da Naira biliyan 21.70 da biliyan N42.27 a shekarar 2012 da 2013 akan hanyar Neja Delta ta Gabas zuwa Yamma; Naira biliyan 197 ya tafi hanyar Benin-Ore, Kano-Maiduguri dual carriageway, Enugu-Port Harcourt, Abuja-Abaji-Lokoja da babban titin Apapa-Oshodi.

Titin jirgin ƙasa daga Legas zuwa Kano, Fatakwal-Maiduguri ya laƙume Naira biliyan 110.78, kamar yadda gwamnati ta kashe Naira biliyan 2.5 wajen lura da ayyukan cikin shekaru biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *