Ƙarya ita ce musabbabin yawan mutuwar aure (1)

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Ƙarya fure take… Wannan karin maganar dai ta daɗe tana yawo, Kuma gaskiya ne komai daren daɗewar ƙarya, gaskiya na tafe.
Ƙarya ce yanzu ta yi yawa cikin duniyar nan. Babu yara, babu manya, kowa so yake ya yi gwaninta ga ɗanuwan zamansa.

Zawarci:
Idan an ambaci wannan kalmar an san me take nufi. Saboda yawan mutuwar aure yanzu da ya yi yawa. zawarawa sun cika gari, ga auren suna so amma ƙarya ta yi wa masu neman auren yawa. Sai sun ƙyalla sun ga mai maiƙo, kuma an tabbata daga inda ta fito akwai maiƙo, sai su biya da cewa suna so. Amma idan an ba ta da shi to yau ƙarya ce, gobe ma haka. A yi ta soyayya ba ji, ba gani, suna ɓata wa juna lokaci. Daga mace ta yi maganar aure, sai ya gudu. A yi ta ganin ita ce maƙaryaciya, ko kuma ba ta son auren. Shikenan an ajiye mata lamba ta ɓatanci, ko a ce tana soyayya da ɗan cikinta .

Kalmar zawarci an daɗe da yi mata baƙar shaida. Mata suna shan wuya. Duk mutuncin mace, duk kamun kanta, da zarar ta fito gidan aure, to fa shikenan sata tata, maita tata. Ba a mata uzirin rayuwa a yau. An fi ɗaukar ta a wacce ba ta son zaman aure. An fi ɗaukar kawai ba ta da kirki, mugun hali ne da ita shi ya sa ta kasa zaman aure. Ba a yi wa namiji wannan shaidar, sai dai ita mace ita ce ka]ai mara kirki.

Daga ta fara zawarci, abinda namiji zai ɗauka, ta banza ce. Sai ya lallaɓo mata da maganganun banza, kamar bai ajiye mace a gida ba. Ko mantawa yake shi ma yana da ƙanne ko mata ko yayye mata? Idan ba ta amince da buƙatarsa ba, to sai ya biya da mugun nufi. Ko’ina ya zauna ya aibata ta. Ya ilahi, me ya sa ake manta kowa da ƙaddararsa? 

Kowacce mace ba ta son ta rabu da mijinta da yaranta sai dole, wallahi. Ba a wa mata uzirin dalilin mutuwar aure. Ba a ma bincike kawai gani ake auren ne ba ta so.

Zaman gida ya kama mace, a bar ta da yara, ba ruwan mijin nan da haƙƙin yaransa. Kawai ya sakarwa mace ta yi masa bautar yaran. Da ma kamar neman kai yake da yaran. Idan tana son rayuwarsu ta inganta, su taso da ilimi da biyayya, to fa ta tafi da abunta. Muddin ta bari to labari ya canza. Idan kuma ta tafi da su, nan ma dai nauyin ne, idan ba ta da aikin yi ko sana’a. Haka za tai ta haƙuri da abin da aka ba su.

Zaman gida fa sai dole. Da ne aka ji daɗi hankali yana kwance, iyaye za su kula da ‘yarsu kuma su kula da jikokinsu. Amma yanzu ina! Ita za ta nema musu abinci, ita za ta nema musu na sabulu, omo, da sauransu.

Mata na ganin rayuwa. Amma a kullum abin da ake hange, su ne marasa son zaman lafiya. Ba uwar da za ta tara yara fiye da uku, da ta zubar da su da gangan ta bar su. Wasu da yawa rashin kulawar da suke samu ne daga maza ke sa su haƙura da zaman gidansu da yaransu. Kuma idan sun koma gidan iyayensu, nan ma ba su huta ba da surutu mutane. Abun da ban gane ba, me ya sa maza ba sa tunanin ƙaddara ne ? Duk yadda mace ta so zama gidanta, wallahi idan Allah bai amince ba, babu yadda za ta yi.

Maimakon a bi ta da addu’a da ban baki, sai a bita da surutu kala-kala. Wani ma ko gaisawa da ba sa yi. Amma ganin aurenta ya mutu, sai ka ga shi ne gaba wajen ba da shaidar ba ta da mutunci. To gara ta lallaɓa, ta samu mijin. Shi kuma ya zo da yaudara, eh mana. ringi]i-ringi]i za a yi magana, sai ta neme shi ta rasa, babu wani dalili.

Wasu mazan kuma, daga sun ji tana da yara, sai ta neme su ta rasa. Masu ƙarfin hali ne ma za su iya ba ta amsa. Idan tana so ya zauna da ita, ta mai da yara, ko kuma to ba ruwansa da tallafa mata. Don ba yaransa ba ne. Ko kuma su raba cefane. Wannan ma an samu ne daga masu adalci. Shi ya sa za a ga mata sun yi yawa. Ba wai auren ne ba sa so ba. A’a, rashin wanda zai riƙe su tsakani da Allah ne babu. Shi ya sa ake ganin matan ba aure. wasu kuma daga matan ne za su ɗauki buri su rataya wa kansu.

Idan namiji bai da kuɗi ko babbar mota, ko wani abu na jin daɗi, sai ta ce ba za ta shiga gidan wahala ba. Ya ilahi, mata idan dai ba matsala za su jawo wa kansu ba, me zai kawo zancen ga irin mijin da za ki zauna da shi ? Matan yanzu sun yi yawa. Ga ‘yan mata ma da ba su yi aure ba,  sun kusa ninka zawarawa. To ya ake so a yi? Kowa ya ɗora wa kansa son Duniya, shi ya sa ko ake danƙare.

Za mu ci gaba a makon gobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *