Ƙasar Sin ta yi kira da a taimakawa ƙasashe masu tasowa don inganta ƙarfinsu na yaƙi da ta’addanci

Daga CMG HAUSA

Jiya ne, zaunannen wakilin ƙasar Sin a MƊD Zhang Jun ya yi jawabi a yayin taron bainar jama’a da kwamitin sulhu na MƊD ya kira kan “Barazanar ayyukan ta’addanci ga zaman lafiya da tsaron ƙasa da ƙasa”, inda ya bayyana matsayin ƙasar Sin, game da yaki da ta’addanci, kana ya yi kira da a mai da hankali kan taimakawa ƙasashe masu tasowa, musamman ƙasashen Afirka, wajen inganta ƙarfinsu na yaki da ayyukan ta’addanci.

Zhang Jun ya ce, rahoton da babban sakataren MƊD ya fitar na nuna cewa, yankuna biyu cikin uku da masu da’awar kafa “Daular Musulunci” suka fi gudanar da ayyukansu, suna Afirka ne.

Don haka, ya kamata, ƙasashen da ke wajen yankin, su ƙarfafa hulɗa da hadin gwiwa da ƙasashen Afirka, tare da tattauna yadda za a warware ƙalubalen da ake fuskanta a fannin dabaru, da kuɗi da ƙarfin ayyukan yaki da ta’addanci da ƙasashen Afirka suke fuskanta ƙarƙashin tsarin MƊD.

Zhang Jun ya ƙara da cewa, ƙasar Sin ta taimaka wa ƙasashe masu tasowa, ta hanyar shiga a dama da ita a haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa kan yaƙi da ta’addanci, musamman ƙasashen Afirka, wajen inganta ƙarfinsu na rigakafi da yaki da ayyukan ta’addanci.

Bugu da ƙari, ƙasar Sin za ta ci gaba da ba da taimako da goyon baya ga ƙasashen da ke kan gaba wajen yaƙi da ayyukan ta’addanci irinsu Afirka da yankin tsakiyar Asiya, domin kara ƙarfinsu na yaki da ta’addanci, ta hanyar ɗaukar matakai na zahiri, da ba da gudummawa wajen tinkarar barazanar ayyukan ta’addanci yadda ya kamata, da kiyaye zaman lafiya da tsaro a yankin.

Fassarawar Ibrahim Yaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *