Ƙungiyoyi sun bayyana shiyyar da ya dace ta fitar da Shugaban Majalisar Dattawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gamayyar ƙungiyoyin da ke sha’awar tsoma baqi a harkokin siyasa a arewa maso yamma, ‘Rescue North West APC Group’ ta ce, ta raba gardama kan kujerar Shugaban Majalisar Dattawa.

An ruwaito gamayyar ƙungiyoyin na cewa shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya ce ta cancanta ta samu kujerar shugaban majalisar dattawa ta 10 da za a kafa.

A cewarsu, ya kamata a baiwa shiyyar wannan kujera saboda ta ba da gudummuwar tulin ƙuri’u, waɗanda suka taimaki Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya kai ga nasara a zaɓen 2023.

Bayan taron da ƙungiyoyin suka gudanar a jihohin Katsina, Kaduna, Kano, Jigawa, Kebbi da Sakkwato, sun cimma matsayar goyon bayan Sanata Barau Jibrin.

Wannam matsaya na ƙunshe a wata sanarwa da Kodinetan gamayyar ƙungiyoyin, Muktar Dahiru-Gore, ya rabawa manema labarai ranar Laraba.

Wani sashin sanarwan ya ce, “Arewa ta yamma ta ba da gagarumar gudummuwar quri’u da suka taimaka wa jajirtaccen shugaban ƙasarmu mai jiran gado, Asiwaju Bola Tinubu, ya lashe babban zaɓen 2023.”

“Shiyyar ce ta bai wa jam’iyyar APC kaso 30 cikin 100 na ƙuri’un da suka ɗaga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya ci zaɓe.”

“Saboda haka muna kira ga kwamitin gudanarwa da shugaban APC, Abdullahi Adamu, da sauran masu kishi, a baiwa arewa maso yamma kujerar Shugaban Majalisar Dattawa.”

“Haka nan bayan miƙa wa shiyyar kujerar, a bai wa Sanata Barau Jibrin, wada ya fi sauran gogewar aiki daga shiyyar arewa maso yamma. Ya koma Sanata karo na uku kenan.”