Ɗan takarar majalisa a jam’iyyar APC ya mutu a hatsarin mota

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan takarar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Nsukka/Igbo-Eze ta kudu ta Enugu a jam’iyyar APC, Ejikeme Omeje, ya rasu a wani hatsarin mota.

Omeje ya mutu ne a kan titin Eden Ani/Nsukka, kusa da otal ɗin El-Rina, Nsukka ranar Talata.

Jaridar Blueprint ta tattaro cewa, yana tuƙi shi kaɗai a kan titin Erina-Edem Ani, kwatsam sai motarsa ta shiga cikin daji inda motar ta yi karo da wata bishiya a kan hanyar.

An garzaya da Omeje asibiti inda ya rasu sakamakon munanan raunuka da ya samu a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *