Ɗangote ya samu lambar girmamawa saboda tallafin Gidauniyarsa ga harkar lafiya

Daga AMINA YUSUF ALI

Hamshaqin ɗan kasuwa, babban shugaban gudanarwa na rukunin kamfanoni da masana’antu Ɗangote, Aliko Ɗangote ya amshi lambar yabo daga shugaban ƙasar Nijar, Mohamed Bazoum a babban birnin garin, Yamai (Niamey).

Ita dai wannan kyauta wacce take tafe da shaidar girmamawa wacce aka ba wa Ɗangote a birnin Niamey babban birnin Nijar ɗin an ba wa Ɗangote ne saboda hidima wa harkar lafiya a jamhuriyar Nijar da Gidauniyarsa ta Ɗangote (ADF) take yi. Sannan kuma don yaba wa irin taimakon da attajirin yake yi wa al’ummar.

Idan za a iya tunawa, da ma gidauniyar Ɗangote ta ADF ta daxe tana kawo ɗauki a ɓangarorin kiwon lafiya da alluran riga-kafi a jamhuriyar Nijar da ma maƙwabtan ƙasashe wato Nijeriya da Chadi.

A wani labarin kuma an rawaito cewa, gidauniyar ADF tare da gidauniyar Bill & Melinda Gates Foundation (BMGF) da ta GAVI sun rattaba hannu a kan takardar fahimtar juna (MoU) tare da gwamnatin Nijar don haɗa gwiwa wajen ingantawa da faɗaɗa shirin gangamin riga-kafi a johohin Diffa, Maraxii and Zinder waɗanda suka yi iyaka da qasar Nijeriya da kudancin ƙasar.

Rahotanni sun nuna cewa, Biloniya attajirin ya samu lambar yabon ne musamman saboda gudunmowoyin da ya ba wa ƙasar a lokuta da dama kamar, Tallafin Dala $500,000 don yaƙi da Annobar ciwon sanƙarau da ta taɓa ɓarkewa a garin, Naira miliyan 250 don tallafin abinci ga yan gudun hijira da waɗanda suka ɓace, sai Dala miliyan guda don tallafawa da bunƙasa riga-kafi a dai johohin guda uku wato, Diffa, Maradi da kuma Zinder.

Idan ba a manta ba, ƙungiyar WHO da ma a baya ta karrama gidauniyar Ɗangote da BMGF da lambar yabo a kan gudunmowarsa wajen nasarar fatattakar cutar shan inna daga Nijeriya da Afirka, a watan Agustan shekarar 2020. Garuruwan da aka samu nasarar sun haɗa da Bauchi, Borno, Kaduna, Kano, Sokoto da kuma Yobe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *