23
Feb
Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya buƙaci takwararnsa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, da ya fito ya bai wa 'yan Nijeriya haƙuri game da furucin da ya yi na goyon bayan Fulani makiyaya su riƙa amfani da bindiga wajen kare kansu. Ortom ya buƙaci haka ne yayin taron manema labarai da ya gudana a Makurdi a Litinin da ta gabata inda ya ce akwai buƙatar Gwamna Bala ya bada haƙuri domin sanyaya zukatan waɗanda suka rasa 'yan'uwa sakamakon ayyukan ɓatagarin Fulani makiyaya. Kazalika, Ortom ya buƙaci Gwamna Bala da ya yi koyi da takwarorinsa na Kano da…