25
Feb
Daga BASHIR ISAH An gudanar da jana'izar jami'an sojin saman nan su 7 da suka rasu a haɗarin jirgin sama da ya auku a Abuja a Lahadin da ta gabata. Jami'an da lamarin ya shafa sun cim ma ajalinsu ne bayan da jirginsu, ƙirar Beechcraft King Air 350, ya faɗo a ƙauyen Bassa daura da Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, bayan da suka tashi da nufin zuwa aiki a jihar Neja. Mai Magana da Yawun Rundunar Sojin Sama na Nijeriya, Air Vice Marshal Ibikunle Daramola ya ce jirgin ya fuskanci matsalar inji kafin aukuwar haɗarin. Cikin waɗanda suka…