03
Apr
Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Kula da Walwalar Alhazai ta Jihar Kano, ta ce ta ƙaddamar da shirin allurar rigakafin cutar korona ga maniyyatan Hajjin 2021 a jihar inda ta soma bada allurar ta kan ma'aikatanta. A wata sanarwa da ta fitar ta hannun jami'arta ta hulda da jama'a, Hadiza Abbas Sunusi, hukumar ta ce ta soma gudanar da shirin ne a Larabar da ta gabata inda aka buɗe fagen yin allurar da fara yi wa Sakataren Hukumar, Muhammad Abba Dambatta. A cewar Sakataren, an ƙaddamar da shirin yin allurar ne domin cika sharaɗin da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta…