Month: April 2021

Ƙa’idojin Azumin Ramadan

Ƙa’idojin Azumin Ramadan

Daga RIDWAN SULAIMAN Da sunan Allah Mai Rahma Mai Jinƙai ‘Yan’uwa maza da mata a Musulunci, huɗubarmu ta yau za ta yi magana ne a kan ƙa’idojin da ke tattare da azumin Ramadan. ‘Yan’uwa maza da mata a Musulunci, yanzu abin da ya rage tsakaninmu da Ramadan wasu ‘yan kwanaki ne, don haka ya kamata mu tunatar da kawunanmu dangane da ƙa’idojin da Ramadan ke tattare da su domin samun tarin sakamako a watan da ke zuwa sau guda a shekara - wa ya sani ko wannan ya zama shi ne Ramadan na ƙarshe a wannan rayuwa! An farlanta yin…
Read More
Koriya ta Arewa ta janye daga gasar Olympics saboda tsoron cutar korona

Koriya ta Arewa ta janye daga gasar Olympics saboda tsoron cutar korona

Daga WAKILINMU Koriya ta Arewa ta bada sanarwar ba za ta halarci gasar Olympics da aka shirya gudanarwa a Ƙasar Tokyo ba a cikin wannan shekara saboda dalili na neman kare 'yan wasanta daga kamuwa da cutar korona. Koriya ta Arewa ta ce na musamman ta ɗauki wannan mataki domin kare 'yan wasanta gudun kada su harbu da cutar korona. Wannan mataki da ƙasar ta ɗauka ya katse wa Koriya ta Kudu damar da ta hango na yin amfani da gasar wajen tattaunawa da takwararta Koriya ta Arewa game da abin da ya shafi kan iyaka. A 2018 ƙasashen biyu…
Read More
Al’ummar Arewa-maso-gabas sun roƙi Buhari da ya inganta tsaron yankinsu

Al’ummar Arewa-maso-gabas sun roƙi Buhari da ya inganta tsaron yankinsu

Daga UAMR M. GOMBE 'Yan gudun hijira a yankin Arewa-maso-gabas sun roƙi gwamnati da ta taimaka ta maido da zaman lafiya a yankinsu domin ba su damar komawa gidajensu don ci gaba da rayuwa kamar yadda suka saba a can baya. 'Yan gudun hijirar sun koka kan yadda rikicin Boko Haram ya ɗaiɗaita su tare da jefa su cikin mawuyacin halin rayuwa, lamarin da ya sa suke shakku kan ko gwamnatin za ta iya maida su matugunansu na asali. Wata sanarwa da 'yan gudun hijirar suka fitar a ƙarkashin Taron 'Yan Gudun Hijira na Yankin Arewa-maso-gabas wadda Manhaja ta mallaki…
Read More
Imo: Yadda IPOB ta kai hari kan gidan yari da hedikwatar ‘yan sanda

Imo: Yadda IPOB ta kai hari kan gidan yari da hedikwatar ‘yan sanda

Daga WAKILINMU 'Yan Ƙungiyar Jama'ar Biafra (IPOB) sun kai mummunan hari kan ofishin 'yan sanda da kuma gidan yari a Owerri babban birnin jihar Imo, inda suka yi sanadiyar tserewar fursunoni da dama 'Yan ƙungiyar wanda da ma ana zarginsu da kashe jami'an tsaro a shiyyar Kudu-maso-gabas, sun kai harin ne ta hanyar banka wuta a gine-gine da motoci da sauran kayayyaki. Majiyar Manhaja ta ce maharan sun yi amfani da abubuwa masu fashewa da kuma bindigogi wajen kai harin. Ta ci gaba da cewa an ji fashewa mai ƙara da kuma harbe-harben bindiga a yankin. Yayin harin, wasu daga…
Read More

Kaduna: ‘Ba mu wakilta kowa don sasantawa da ‘yan fashi ba’ – Aruwan

El-Rufai Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Jihar Kaduna ta sha alwashin hukunta duk wanda ta kama yana sasantawa da 'yan fashi ko 'yan ta'adda a jihar. Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Lahadin da ta gabata. Kwamishinan ya ce Gwamnatin Kaduna ba ta wakilta kowa ba don shiga tsakaninta da 'yan fashi, tare da ƙaryata rahoton da ke cewa Gwamnatin Nasir El-Rufai ta naɗa wasu wakilai domin tattaunawa da masu aikata muggan laifuka a jihar. Sanarwar Kwamishinan ta buƙaci 'yan jihar da su kai rahoton…
Read More
Gumi da Obasanjo sun yi ganawar sirri

Gumi da Obasanjo sun yi ganawar sirri

Daga FATUHU MUSTAPHA Fitaccen malamin Islman nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi wata ganawar sirri tare da Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta babban birnin jihar Ogun, a Lahadin da ta gabata. Wata majiya ta kusa da taron, ta ce Gumi ya zaɓi ganawa da Chief Obasanjo ne kasancewarsa na mai faɗa a ji a cikin ƙasa kuma wanda al'umma ke girmamawa. Malamin ya labarta wa Obasanjo ziyarar da ya kai wa Fulani masu fashi a Arewacin ƙasa da zummar gwamnati ta yi wa yanayin kyakkyawar fahimta da kuma yin aiki da shawarwarin da…
Read More

Kada ‘yan Nijeriya su yanke tsammanin samun daidaiton Nijeriya – Osinbajo

Osinbajo Daga UMAR M. GOMBE Mataimakin Shugaban Ƙasa Professor Yemi Osinbajo, ya buƙaci 'yan Nijeriya da su zamo masu kyautata zato tare da fatan harkoki za su daidaita a ƙasa. Osinbajo ya faɗi haka ne yayin wata ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala ibadar Easter a mujami'ar Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a Lahadin da ta gabata. A cikin sanarwar da hadiminsa kan sha'anin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Laolu Akande ya fitar, Osinbajo ya ce yana da yaƙinin rahma da albarkar Ubangiji za su lulluɓe Nijeriya. Sanarwar mai taken 'Saƙon bikin Easter na Osinbajo zuwa…
Read More
Matawalle: APC ta yi babban kamu a Zamfara

Matawalle: APC ta yi babban kamu a Zamfara

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya kammala shirin sauya sheƙa daga jam'iyyarsu ta PDP zuwa APC inda ake sa ran shugaban riƙo na APC, Mai Mala Buni ya gabatar da shi ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna mai yiwuwa a kammala komai idan tawagar Gwamnatin Tarayya ta ziyarci Zamfara a ranar Talata domin jajanta wa gwamnan game da ibtila'in gobarar kasuwa da ya auku kwannan nan a jihar. Tun ba yau ba, wasu gwamnoni masu ci tare da tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yerima, na daga cikin gaggan 'yan siyasar da…
Read More
Za a fara rajistar masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni

Za a fara rajistar masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za a ci gaba da aikin rajistar katin masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni, 2021. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a taron da ya yi da su a hedikwatar hukumar a Abuja a ranar Alhamis. Mahmood ya ce, “Bayan mun duba waɗannan matsaloli da matakan da mu ka ɗauka don magance su, yanzu hukumar ta kai matsayin da za ta iya bayyana Litinin, 28 ga Yuni, 2021 a matsayin ranar da za mu koma mu ci gaba…
Read More