03
Jun
Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta ce amfani da kekuna a matsayin hanyar sufuri zai taimaka wajen rage yawan haɗurra da kuma cinkoson abubuwan hawa a hanyoyi. Shugaban hukumar a jihar Filato, Alphonsus Godwin, shi ne ya bayyana haka a wajen wani gangamin masu tuƙa kekuna da aka shirya a Jos albarkacin Bikin Ranar Keke ta Duniya na 2021. A cewar jami'in, baya ga rage yawan aukuwar haɗurra, haka nan amfani da keke na taimako wajen inganta lafiya da kuma tabbatar da yanayi mai cike da lafiya, don haka ya shawarci al'ummar Filato da kewaye…